Yan bindiga sun kashe Sajen na yan sanda tare da warewa da bindigarsa a Owerri

Yan bindiga sun kashe Sajen na yan sanda tare da warewa da bindigarsa a Owerri

- Wasu yan binda sun sake kai wani harin a garin Owerri inda suka kashe wani Sajen na yan sanda, mai suna Christian Nnamani

- Rahotanni sun bayyana cewa yan bindigar sun arce da bindigar dan sandan kirar AK47, tare da harbin wani da yazo wucewa

- Kwamishinan yan sanda na jihar, Dasuki Galadanchi, ya bada umurnin gaggauta bincike don kama wadanda suka aikata laifin kisan

Kasa da awannai 48 da wasu yan bindiga suka kashe wani limamin Katolika, Rabaran Jude Egbom, a garin Kwerre, karamar hukumar Nkewere da ke jihar Imo, rahotanni sun nuna cewa wasu yan binda sun sake kai wani harin a garin Owerri inda suka kashe wani Sajen na yan sanda, mai suna Christian Nnamani.

Rahotanni sun bayyana cewa yan bindigar, wadanda suka arce da bindigar dan sandan kirar AK47, sun kuma harbi wani da yazo wucewa ta inda suke aikata aika aikar.

Legit.ng ta samu rahoto cewa lamarin ya afku ne da misalin karfe 9 na safiyar ranar talata a sha-tale-talen Control Post, da ke daura da shelkwatar Cocin Cathedral, da ke Owerri.

KARANTA WANNAN: Okonjo-Iweala ce ta tsamo Nigeria daga kogin basussukan kasashen waje - Amina Muhammad

A ranar Laraba, wani wanda lamarin ya auku a gaban sa ya shaidawa manema labarai cewa lokacin da lamarin ya auku akwai jami'an rundunar yan sanda da ke aiki a kan titin.

Yan bindiga sun kashe Sajen na yan sanda tare da warewa da bindigarsa

Yan bindiga sun kashe Sajen na yan sanda tare da warewa da bindigarsa
Source: Depositphotos

Da ya ke tabbatar da faruwar lamarin ta hanyar wayar tarho a ranar Laraba, jami'in hulda da jama'a na rundunar yan sanda a jihar, SP. Andrew Enwerem, ya ce bayan da yan bindigar suka kashe dan sandan, su gudu da bindigar sa.

Kakakin rundunar yan sanda ya ce wanda ke wucewa akan hanyar da yan bindigar suka harba, an garzaya da shi cibiyar lafiya ta gwamnatin tarayya da ke Owerri, inda a yanzu ya ke samun kulawar likitoci.

Emwerem ya ce tuni rundunar yan sanda ta fara bincike kan lamarin, yana mai cewa kwamishinan yan sanda na jihar, Dasuki Galadanchi, ya bada umurnin gaggauta bincike don kama wadanda suka aikata laifin kisa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel