Hadimin Buhari yaga baiken majalisar Tarayya kan kudaden da INEC ke bukata don 2019

Hadimin Buhari yaga baiken majalisar Tarayya kan kudaden da INEC ke bukata don 2019

- Majalisar dattawa basu ta iko akan yanda za'a samo kudin zabe

- Kudin zai kara yawan kasafin kudin shekarar

- In har bazasu duba kasafin kudin wasu cibiyoyin ba, toh bai kamata su tambaya inda za a samo su ba

Hadimin Buhari yaga baiken majalisar Tarayya kan kudaden da INEC ke bukata don 2019

Hadimin Buhari yaga baiken majalisar Tarayya kan kudaden da INEC ke bukata don 2019
Source: UGC

Mai taimakon shugaban kasa, Ita Enang, yace kwamitin majalisar dattawa akan harkokin zabe basu da ikon fadin inda za'a nemo kudin zaben 2019.

Mista Enang, hadimin shugaban kasa na musamman akan harkokin majalisar dattawa ya sanar da ofishin dillancin labarai a zauren su dake Abuja.

Kwamitin kula da harkokin zabe na majalisar dattawa, a ranar 30 ga watan Augusta ta shawarci INEC da ta samo Naira biliyan 143 na zaben 2019 daga gurin Special intervention programme.

Shugaban kwamitin, Suleiman Nazif, yace sun bada shawarar ne don saukakewa da hana kara yawan kudin da za'a kashe a 2018.

DUBA WANNAN: Kwankwaso yace yayi kuskure a 2015

Amma Mista Enang yace mahukuntan basu da hurumin bada shawara akan inda za'a samo kudin domin kamata yayi kawai su amince kawai.

Idan har basu damu da kasafin kashe kudin wasu cibiyoyin irin su yan sanda, immigration da sauransu ba, toh kuwa basu da damar tambayar Onda za a samo kudin, Inji shi Enang.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel