An raunata jama'a a harin ta'addanci a birnin Paris na Faransa

An raunata jama'a a harin ta'addanci a birnin Paris na Faransa

- An kama wani Dan kasar Afghanistan a Paris

- Ya kai hari, inda ya raunata mutum 7

- Ba a cikin hayyacin shi yake ba, aikin kwaya ne

An raunata jama'a a harin ta'addanci a birnin Paris na Faransa

An raunata jama'a a harin ta'addanci a birnin Paris na Faransa
Source: Depositphotos

Wani Dan kasar Afghanistan ya kai hari a kasar Paris. Harin da ya bar mutane 7 da rauni, wanda ya hada da masu yawan shakatawa 3.

A yanzu haka hukumar yan sanda na binciken mutumin. Mutumin mai shekaru kusan talatin a duniya yaje arewa maso gabas din kasar da wuka a ranar lahadi inda ya raunata mutane 7.

DUBA WANNAN: NERC ta tsawatar wa NEPA

Mutanen da ke gurin ne suka bishi da jifa da kwallo, wani kuma yasa karfe ya buge hannun shi da ke dauke da wutar. A take ya fadi kasa warwas. Inda daga baya yan sanda suka zo, suka wuce dashi asibiti.

Wani ganau ba jiyau ba mai suna Buoadjema yace da alama mutumin ba a hankalin shi yake ba, don koda ya taho da wukar bai ce komai ba. Koda aka bishi bai yi ihu ba, har aka buge shi.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel