Okonjo-Iweala ce ta tsamo Nigeria daga kogin basussukan kasashen waje - Amina Muhammad

Okonjo-Iweala ce ta tsamo Nigeria daga kogin basussukan kasashen waje - Amina Muhammad

- Amina Mohammed, ta ce Ngozi, ta tsamo Nigeria daga kogin basussukan da kasashen waje ke binta, amma a yanzu kasar ta dawo tsundum a cikin basussukan

- Ta ce akwai bukatar MDD da IMF su tattauna kan hanyoyin farfado da tattalin arziki, da kuma hanyoyin bunkasa rawuyar al'umma

Amina Mohammed, mataimakiyar babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya (UN), ta ce Ngozi Okonjo-Iweala, wacce tarike mukamin ministar kudi har sau biyu, ta kwashe shekaru don tsamo Nigeria daga kogin basussukan da kasashen waje ke binta, amma a yanzu kasar ta dawo tsundum a cikin basussukan.

Da take jawabi a wani taron tattaunawa tsakanin MDD da kamfanin IMF, a ranar Talata, tsohuwar ministar muhalli a Nigeria, ta bayyana damuwarta dangane da hauhawar kudaden bashin da Nigeria ke ci dama sauran kasashen Afrika.

Ta ce akwai bukatar MDD da IMF su tattauna kan hanyoyin farfado da tattalin arziki, da kuma hanyoyin bunkasa rawuyar al'umma.

KARANTA WANNAN: APC ta karyata rahoton EIU, HSBC na cewar tattalin arziki zai karye idan Buhari ya zarce

"Samar da kayyaki da kudade na al'umma na da matukar amfani, haka ma bangarorin da ke zama da kansu. Sai dai ina tsoron cewa har yanzu bamu samo maganin matsalolinmu ba, sai dai ina sa ran cewa hadakar da mukayi zata samar da kofar da zamu samo abubuwan da muka rasa" a cewar ta.

Okonjo-Iweala ce ta tsamo Nigeria daga kogin basussukan kasashen waje - Amina Muhammad

Okonjo-Iweala ce ta tsamo Nigeria daga kogin basussukan kasashen waje - Amina Muhammad
Source: Depositphotos

Amina Muhammad ta ci gaba da cewa: "A kan hanyata daga birnin New York, wasu daga cikin matsalolin da muka tattauna akan su a taronmu da China, da kuma rahotannin da muka tattara; mun gano cewa adadin basussukan abun daga hankali ne, ina nufin duba da irin wahalar da Ngozi Okonjo-Iweala ta sha wajen cire Nigeria daga kogin basussukan da ta shiga.

"Ta shafe shekaru don samun nasarar hakan, sai dai yanzu mun koma baya a kasata, basussukan da ake binta abun damuwa ne, ko da ya ke ko ina ma hakan take faruwa. Shin ina muka dosa ne Afrika?

"Ina tunanin akwai bukatar mu zauna mu tattauna akan muhimman abubuwan da ke gabanmu musamman akan tattalin arziki; dole ne mu ga nasarar hakan, domin kawai bukatar magance wannan matsalar fiye da kullum, muna kan aiki don tabbatar da hakan"

A tattaunawar da Christine Lagarde, Manajan Daraktar IMF, Mohammed ta yarda da Lagarde cewa Okonjo-Iweala ta yi matukar kokari wajen cire Nigeria daga kangin basussukan da ake binta a 2006.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Tags:
Mailfire view pixel