Tafiyar chanjin 2015 babban kuskure ne - Kwankwaso

Tafiyar chanjin 2015 babban kuskure ne - Kwankwaso

Tsohon gwamnan jihar Kano kuma dan takarar kujerar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Dr. Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana cewa chanjin da shi da sauran wadanda suka marawa Shugaban kasa Muhammadu Buhari baya suka bi a 2015 shine babban kuskuren da suka yi.

Ya bayyana hakan a ranar Laraba, 12 ga watan Satumba da yake jawabi ga yan PDP na jihar Niger da magoya bayansu a sakatariyar jam’iyyar dake Minna cewa yawan Magana da aka tayi akan chanji ai kawo komai ba face yunwa, kashe-kashe da kuma rashin aiki.

Da yake Magana akan batun tsayar da dan takara guda da shugabannin jam’iyyar sun nema, Kwankwaso ya bayyana cewa ba zai amince da hakan ba amma duk wanda yayi nasarar lashe zaben fidda gwani zai samu cikakken goyon bayansa.

Tafiyar chanjin 2015 babban kuskure ne - Kwankwaso

Tafiyar chanjin 2015 babban kuskure ne - Kwankwaso
Source: Depositphotos

Ya cigaba da bukatar yan Najeriya da su bude koffinsu tare da rungumar yan kungiyar kwankwasiya inda ya kara da cewa “mun san mutunci da aiki”.

KU KARANTA KUMA: Dariye zai mayar da fam dinsa na takaran sanata a gobe – APC Plateau

Da farko dai Kwankwaso ya gana da tsohon shugaban kasar Najeriya a mulkin sojoji, Janar Ibrahim Badamasi Babangida cikin sirri.

Dan takaran kujerar shugaban kasar ya bayyana ne cikin shigarsa ta kwankwasiya wato farin kaya da jar hula, a Minna babbar birnin jihar Niger.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel