Dariye zai mayar da fam dinsa na takaran sanata a gobe – APC Plateau

Dariye zai mayar da fam dinsa na takaran sanata a gobe – APC Plateau

Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) reshen jihar Plateau ta tabbatar da cewa sanata mai wakiltan Plateau ta tsakiya a majalisar dokokin kasar, Joshua Dariye ya yanki fam din takara a jihar.

Jam’iyyar ta kuma bayyana cewa, tsohon gwamnan na jihar Plateau na shirin dawo da fam din imam a sakatariyar jam’iyyar na kasa ko kuma a sakatariyar jam’iyyar na jihar.

Jam’iyyar ta bayar da tabbacin ne ta hannun sakatarenta, Alhaji Bashir Musan Sati a wata hira da jaridar Daiyl Trust a gidansa dake Jos a ranar Laraba, 12 ga watan Satumba.

Dariye zai mayar da fam dinsa na takaran sanata a gobe – APC Plateau

Dariye zai mayar da fam dinsa na takaran sanata a gobe – APC Plateau
Source: Depositphotos

Ku tuna cewa, Justis Adebukola Banjoko ta babbar kotun tarayya dake Abuja ta yankewa Dariye daurin shekaru 16 gidan yari bayan an same shi da hannu dumu-dumu wajen karkatar da naira biliyan 1.6 na jihar Plateau lokacin da yake gwamna tsakanin 1999 zuwa 2007.

An zabi Dariye a matsayin sanata mai wakiltan Plateau ta tsakiya a 2015 a karkashin jam’yyar Peoples Democratic Party (PDP) amma ya sauya sheka zuwa APC mai mulki a 2017.

KU KARANTA KUMA: IGP Idris ya gurfana a gaban majalisar dattawa kamar yadda ta bukata – Tsohon IGP Abba

Alhaji Sati yayi bayanin cewa tuni Dariye ya siya fam din takara kuma zai mayar da shi a gobe Alhamis ranar karshe da aka sa na karban fam din.

Yace “Lamarin Dariye ba sabon abu bane dan siyasa yayi takara yayinda yake gidan yari, don haka, tsohon mataimakin gwamnan jihar Osun, Otunba Iyiola Omisore ya lashe kujerar ssanata a zaben 2003 yayinda yake gidan yari.”

Hakan na zuwa ne bayan kakakin jam'iyyar APC yace bazasu siyarwa mai laifi da fam din takara ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel