Najeriya ba ta taba shugaba wanda bai cancanci jagoranci ba tamkar Buhari - Atiku

Najeriya ba ta taba shugaba wanda bai cancanci jagoranci ba tamkar Buhari - Atiku

A yayin da tsohon Mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar, ke ci gaba da shawagi na yakin neman zabe a kasar nan, ya na kuma ci gaba da suka gami da caccakar gazawar shugaban kasa Muhammadu Buhari akan jagorancin kasar nan.

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya bayyana cewa, kasawar shugaba Buhari ta riƙe wasu muhimman jiga-jigai a jam'iyyar sa ta APC ta tabbatar da haƙiƙanin raunin sa da rashin sani makamar aiki ta fuskar jagoranci da shugabanci.

Atiku wanda ya yi wannan furuci da sanadin kakakin kungiyar yakin sa ta neman zabe, Segun Sowunmi, ya bayyana cewa, yana ci gaba da hanƙoron kujerar shugaban ƙasa kurum da muradin tsarkaketa daka dukkan wani gurbatanci da shugaba Buhari ya jefa ta a ciki.

Kamar yadda shafin jaridar The Punch ya ruwaito, Turakin na Adamawa ya bayyana yadda gazawar shugaba Buhari tayi sanadiyar tabarbarewar wasu al'amurra da suka hadar da rashin aikin yi, zagwanyewar tattalin arziki inda a halin yanzu ta kasance daya daga cikin kasashe mafi afkawa cikin kangin talauci a duniya.

Najeriya ba ta taba shugaba wanda bai cancanta ba tamkar Buhari - Atiku

Najeriya ba ta taba shugaba wanda bai cancanta ba tamkar Buhari - Atiku
Source: Depositphotos

Mista Segun ya ci gaba da cewa, Najeriya ba ta taba samun wani jagora ba wanda ba ya da wata cancanta ta rike kujerar fadar shugaban kasa tamkar shugaba Buhari.

KARANTA KUMA: Sayen Fam din takara na N45m ga shugaba Buhari ya sabawa doka - Ben Bruce

Kakakin kungiyar ya bayyana hakan ne yayin mayar da martani kan furucin shugaba Buhari, inda ya kausasa harshe kan wadanda suka sauya sheka daga jam'iyyar sa ta APC zuwa PDP da cewar 'yan siyasa ne masu rauni da kuma son zuciya.

Jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, a ranar yau ta Laraba shugaba Buhari ya mayar da fam din sa na bayyana kudirin neman takara zuwa ga shelkwatar jam'iyyar sa ta APC dake unguwar Wuse a babban birnin kasar nan na tarayya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Legit

Mailfire view pixel