Dukkan 'yan takarar PDP sun hada kai a kan abu guda - Bafarawa

Dukkan 'yan takarar PDP sun hada kai a kan abu guda - Bafarawa

- Tsohon gwaman jihar Sokoto, Attahiru Bafarawa, ya ce dukkan 'yan takarar shugabancin kasa a PDP sun hada kai domin ganin kawar da APC a 2019

- Bafarawa ya ce adadin mutanen da suke neman takarar shugabancin kasa a PDP ya nuna jam'iyyar tana bunkasa

- Bafarawa kuma ya yi kira da jam'iyyar tayi amfani da tsarin zaben fitar da gwani a maimakon tursasa wa jam'iyyar wanda mutane ba su so

Daya daga cikin masu neman tikitin takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar PDP, Dr. Attahiru Bafarawa, ya ce dukkan 'yan takarar PDP sun hada kansu kan abu guda, kuma itace kawar da gwamnatin APC a shekarar 2019.

Bafarawa ya yi wannan furucin ne a lokacin da ya kai ziyara jihar Edo domin kamfe gabanin babban taron jam'iyyar da za'ayi a watan Oktoban 2018.

Dukkan 'yan takarar PDP sun hada kai a kan abu guda - Bafarawa

Dukkan 'yan takarar PDP sun hada kai a kan abu guda - Bafarawa
Source: Depositphotos

Tsohon gwamnan jihar Sakkwato, ya kuma ce gudanar da zaben fitar da gwani shine abinda ya yi dai-dai da tsarin demokradiya a maimakon shugabanin jam'iyya su tursasa wa sauran mutane dan takarar da dole ne ya kasance shi yafi cancanta ba.

DUBA WANNAN: Obasanjo na neman a halasta amfani da wiwi da sauran kwayoyi a Afrika

Bugu da kari, Bafarawa ya yi alfahari da adadin mutanen da ke neman takarar shugabancin kasa karkashin jam'iyyar PDP, inda ya ce hakan na nuna cewa jam'iyyar tana da farin jini kuma tana kara bunkasa.

Ya kara da cewa dukkan 'yan takarar sun amince za su goyi bayan duk wanda ya yi nasarar samun tikitin takarar a zaben 2019.

"Mun riga munyi shawarar mara wa duk wanda ya yi nasarar samun tikitin jam'iyyar PDP baya kuam za muyi aiki tare dashi.

"Adadin masu neman takarar ba matsala ba ce. Hakan na nuna cewa jam'iyyar na kara girma. Jam'iyyarmu ta jama'a ne kuma kowa na iya shigowa.

"Kan mu a hade ya ke. Za muyi aiki tare domin kawar da jam'iyyar APC daga mulki saboda jam'iyyar matsala ta janyo wa Najeriya." inji Bafarawa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel