Babban malamin Islama na son a rage albashin 'yan siyasa

Babban malamin Islama na son a rage albashin 'yan siyasa

- Wani babban limami a Ilorin, Alhaji Abdullahi AbdulHameed, ya bukaci a rage alashin 'yan siyasa

- Babban malamin ya ce adadin kudaden da 'yan siyasar ke karba a matsayin albashi yana daga cikin abin da ya jefa Najeriya cikin talauci

- Imam AbdulHameed ya ce dole sai 'yan siyasa sun nuna jin kai ga talakawa ta hanyar rage albashinsu muddin ana son rage radadin talauci

Babban limamin Imale da ke Ilorin, Alhaji Abdullahi AbdulHameed, ya bayar da shawarar rage albashin masu rike da mukamman siyasa. Ya ce ya kamata ayi la'akari da halin da mafi yawan jama'a ke ciki a Najeriya na talauci.

Babban malamin Islama na son a rage albashin 'yan siyasa

Babban malamin Islama na son a rage albashin 'yan siyasa
Source: Depositphotos

AbdulHameed ya fadi hakan ne a jiya, 1 ga watan Muharram (Hijrah 1440), yayin wata hira da ya yi da wakilin Daily Trust.

DUBA WANNAN: Obasanjo na neman a halasta amfani da wiwi da sauran kwayoyi a Afrika

A cewar babban malamin, zunzurutun kudaden da suke karba a matsayin albashi ne ya janyo talaucin da ake fama dashi a kasar.

Ya ce idan ministoci, 'yan majalisar tarayyar, kwamishinoni da sauran masu rike da mukamman siyasa suka rage albashinsu, hakan zai kawo saukin talauci sosai a Najeriya.

"A halin yanzu da muke shiga sabuwar shekara, ya dace 'yan siyasar mu tausayawa talakawan da suke mulka. Albashin da shugabanin siyasa ke karba ya yi yawa sosai, musamman 'yan majalisa; babu yadda za'a samu saukin talauci idan aka cigaba a haka," inji AbdulHameed.

A wata rahoton, Legit.ng ta kawo muku cewa tsohon shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo ya shawarci gwamnatocin Afirka su halasta amfani da ganyen wiwi kamar yadda sauran kasashen duniya keyi.

Tsohon shugaban kasan ya fadi hakan bayan kwamitin da ya ke jagoranta kan hanyoyi magance ta'amulli da miyagun kwayoyi a Afirka ta yamma ta kammala binciken ta.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel