IGP Idris ya gurfana a gaban majalisar dattawa kamar yadda ta bukata – Tsohon IGP Abba

IGP Idris ya gurfana a gaban majalisar dattawa kamar yadda ta bukata – Tsohon IGP Abba

Suleiman Abba, tsohon Sufeo Janar na yan sanda ya bukaci Sufeto Janar na yan sanda mai ci a yanzu, Idris da ya amsa gayyatar da majalisar dattawa tayi masa ta hanyar gurfana a gabanta domin kare kansa.

Abba wanda ya yanki fam din takaran sanata mai wakiltan Jigawa ta tsakiya a majalisar dattawa yace babu wanda zai kare shugaban yan sandan sama da shi kansa.

Tsohon shugaban yan sandan zai yi takara ne a karkashin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki.

IGP Idris ya gurfana a gaban majalisar dattawa kamar yadda ta bukata – Tsohon IGP Abba

IGP Idris ya gurfana a gaban majalisar dattawa kamar yadda ta bukata – Tsohon IGP Abba
Source: Depositphotos

Don haka yace yana mai shawartan IGP da ya bayyana a gabansu kamar yadda suka nema.

Legit.ng ta tattaro cewa Suleiman Abba, Sufeo Janar na yan sanda a karkashin gwamnatin Goodluck Jonathan a ranar Litinin, 10 ga watan Satumba ya kaddamar da cewa zai yi takarar kujerar sanata karkashin jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

KU KARANTA KUMA: 2019: Okorocha ya sallami kwamishinoni 13 da hadimai

Abba zai yi takaran kujerar sanata mai wakiltan yankin Jigawa ta arewa wanda a yanzu Sabo Muhammed Nakudu ke rike da shi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel