Bukola Saraki ya mika fam din takarar Shugaban kasa a ofishin PDP

Bukola Saraki ya mika fam din takarar Shugaban kasa a ofishin PDP

Mun ji labari cewa Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki ya cike fam din sa na takarar Shugaban kasa da ya saya kwanaki kuma har ya mika cikakken takardun a Sakatariyar PDP. Saraki yana sa rai PDP ta ba sa tikitin 2019.

Bukola Saraki ya mika fam din takarar Shugaban kasa a ofishin PDP

Saraki ya maida fam din sa na takarar kujerar Shugaban kasa a PDP
Source: Depositphotos

Bukola Saraki ya tabbatar da shirin sa na takarar Shugaban kasa bayan da ziyarci babban ofishin Jam’iyyar PDP inda ya mika fam din sa na shirin takarar kujerar Shugaban kasa a zaben 2019 a karkashin babbar Jam’iyyar adawar.

Shugaban Majalisar Kasar ya shirya fafatawa a zaben fitar da gwani da za ayi kwanan nan inda zai fuskanci irin su Tsohon Mataimakin Shugaban kasa Atiku Abubakar, Ahmad Makarfi da kuma Abokin aikin sa Rabiu Kwankwaso.

KU KARANTA: Saraki yayi wani sabon nadi a Majalisar Dattawan Najeriya

Kawo yanzu dai akwai fiye da ‘Yan takara 10 da ke neman kujerar Shugaban kasa a Jam’iyyar PDP. Tsohon Gwamnan Jihar Kwara Bukola Saraki ya tubure cewa yanzu ya kamata Yankin arewa ta Tsakiya ta fito da Shugaban kasa.

Tuni dai Atiku Abubakar ya nuna cewa babu wani shiri da Jam’iyyar PDP ke yi wajen tsaida ‘Dan takarar Shugaban kasa daga Arewa maso tsakiyar kasar. Sanatoci irin su Jonah Jang da David Mark dai su na cikin masu harin kujerar Buhari.

Jiya ma dai Saraki ya tabbatar da cewa masu neman takarar kujerar Shugaban kasa a karkashin PDP duk sun hadu a Abuja. Har su Aminu Tambuwal, Sule Lamido, Kabiru Taminu Turaki da ma Alhaji Attahiru Bafarawa sun halarci zaman.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel