EFCC na neman jami’an jihar Rivers 4 ruwa a jallo kan zargin zambar N117bn

EFCC na neman jami’an jihar Rivers 4 ruwa a jallo kan zargin zambar N117bn

- Hukumar EFCC na neman jami’an jihar Rivers 4 ruwa a jallo

- Ana zargin jami'an da laifi zamba da wawushe naira biliyan 117 na gwamnati

Hukumar yaki da cin hanci da hana yiwa tattalin arziki zagon kasa (EFCC) ta kaddamar da neman wasu jami’an gwamnatin jihar Rivers guda hudu ruwa a jallo kan zargin hada kai wajen aikata laifi zamba da wawushe naira biliyan 117 na gwamnati da kuma cin zarafin matsayinsu.

Hukumar yaki da cin hanci da rashawar ta wallafa hotuna da sunayen wadanda take neman shafinta na Facebook a ranar Laraba, 12 ga watan Satumba.

EFCC na neman jami’an jihar Rivers 4 ruwa a jallo kan zargin zambar N117bn

EFCC na neman jami’an jihar Rivers 4 ruwa a jallo kan zargin zambar N117bn
Source: Facebook

KU KARANTA KUMA: 2019: Okorocha ya sallami kwamishinoni 13 da hadimai

Jami’an da ake nema sune

1. Fubara Siminayi (daratan kudi na gwamnatin jihar Rivers)

2. Harrisonba Bessi Princewill

3. Lekia V. Bukpor

4. Dagogo Roderick Abere

A halin da ake ciki, Legit.ng ta rahoto a baya cewa Gwamna Nyesom Wike na jihar Rivers ya sha alwashin cewa babu wani jami’in jihar da zai gurfana a gaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa don bincike.

Gwamnan yayi Magana ne bayan hukumar EFCC tayi tambaya game da zargin fitar da naira biliyan 117 da aka yi a shekaru uku da suka gabata.

Gwamnan ya zargi EFCC da ziyasantaar da bincike sannan cewa har sai hukuncin 2007 da ya hana hukumar bincike ya cika, babu wani jami’i da zai gurfana don bincike.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel