APC ta karyata rahoton EIU, HSBC na cewar tattalin arziki zai karye idan Buhari ya zarce

APC ta karyata rahoton EIU, HSBC na cewar tattalin arziki zai karye idan Buhari ya zarce

- APC ta karyata rahoton EIU, HSBC na cewar tattalin arziki zai karye idan Buhari ya sake zama shugaban kasar Nigeria bayan zaben 2019

- Kamar yadda rahoton da kamfanin EIU ya fitar, jam'iyyar adawa ta PDP ce zata lashe zaben 2019, wacce itama zata fuskanci karyewar tattalin arziki

- Jam'iyyar APC ta bukaci yan Nigeria da su kauracewa wannan rahoton domin ba su ne na farko da suka taba yin irin wannan hasashe ba

Jam'iyyar APC ta karyata rahotan sashen kwararru kan tattalin arzikin kasa (EIU) da HASBC, wani kamfani mai harkoki a kasashe kan bankuna da kudade, rahoton da ke cewa zarcewar shugaban kasa Muhammadu Buhari a 2019 zai jawo mummunan karyewar tattalin arzikin Nigeria.

A cikin wata sanarwa da ta bayar a ranar Laraba, dauke da sa hannun Yekini Nabena, Sakataren watsa labarai na jam'iyyar na kasa, APC ta ce rahoton da kamfanin EIU ya fitar, na nuni da cewa jam'iyyar adawa ta PDP ce zata lashe zaben 2019, da cewar gwamnatin gaba zata fuskanci babbar matsalar tsaro.

"Gwamnatin gaba zata fuskanci karyewar tattalin arzikin kasa (bayan zaben 2019) wanda hakan ke nuni da cewa barazanar da tsaro ke fuskanta a kasar zai zarce na yanzu" a cewar rahoton EIU.

Haka zalika rahoton ya bayyana cewa: "Muna kyautata tsammanin samun karuwar matsalolin tsaro, ko da ya ke rundunar soji kwararru ne a wannan bangaren"

APC ta karyata rahoton EIU, HSBC na cewar tattalin arziki zai karye idan Buhari ya zarce

APC ta karyata rahoton EIU, HSBC na cewar tattalin arziki zai karye idan Buhari ya zarce
Source: Depositphotos

Jam'iyyar APC ta bukaci yan Nigeria da su kauracewa wannan "hasashe da rahoton kamfanin" domin sanin su da kuma watsi da su kasancewar ba su ne na farko da suka taba yin irin wannan hasashe ba, a shekarun baya hukumomin kasashen turai sun sha fitar da irin wadannan rahotanni.

KARANTA WANNAN: An cafke wani dalibi yana kokarin yin sata a filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe

A shekarun baya, an fitar da rahotannin cewa kasar Nigeria zata wargaje a 2015, biyo bayan ballewar wasu kabilu da zasu bukaci samun yancin cin gashin kansu.

Sai dai, an doshi akalla shekaru 4 da wucewar shekarar da akayi hasashen zata zamo shekarar rabuwar Nigeria, mai-makon ma kasar ta rabu, sai ma kara dunkulewa da ta ke yi, yayin da gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta maida hankali wajen samar da hadin kai a cikin kasar.

APC ta buga misali da gwamnatocin baya da suka gabata, wadanda aka saci kudaden jama'a, gwamnatocin da suka mayar da wasu hukumomi kamar karnukan farautarsu, irin su hukumar jarabawar share fagen shiga manyan makarantu (JAMB), hukumar tattara haraji ta kasa (FIRS) da kuma hukumar hana fasa kwabri ta kasa (NCS).

Jam'iyyar ta kuma bayyana takaicinta na yadda EIU ta ki lura da irin kudaden da aka kwato daga barayin gwamnati, ta hanyar hukumar EFCC.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel