An cafke wani dalibi yana kokarin yin sata a filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe

An cafke wani dalibi yana kokarin yin sata a filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe

- An gurfanar da wani dalibi, Emnanuel Okoyata, a gaban kotun majistire ta Kuje da ke Abuja, bisa zarginsa da aikata laifuka guda biyu

- Sai dai wanda ake zargi da aikata laifin, ya musanya wannan zargi da ake masa

- Mai shari'a Mr Taribo Jim, ya bada belin wanda ake zargin tare da daga sauraren karar har sai 9 ga watan Oktoba

A ranar Laraba ne aka gurfanar da wani dalibi, Emnanuel Okoyata, a gaban kotun majistire ta Kuje da ke Abuja, bisa zarginsa da laifin kuste a filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe, Abuja bisa aikata laifuka biyu.

An gurfanar da Oyoyata mai shekaru 28 da haihuwa, wanda ke da zama a kauyen Bassa kusa da filin jirgin, da aikata laufkan kutse da kuma kokarin yin sata.

Yar sanda mai shigar da kara, Mrs Doris Okoroba, ta ce jami'an hukumar filin jirgin ne suka kai rahoton hakan ga rundunar yan sanda ta Kuje a ranar 6 ga watan Satumba.

Okoroba ya ce a ranar da aka shigar da rahoton, wanda ake zargin da ya saba aikata munanan laifuka a yankin, ya yi kokarin shiga cikin ginin filin jirgin ta barauniyar hanya.

KARANTA WANNAN: Cin hanci: Sama da N11bn aka kwato daga hannun jami'an rundunar yan sanda a shekaru 2

An gurfanar da dalibi a gaban kotu da aikata laifukan kutse da yin sata a filin jirgin sama

An gurfanar da dalibi a gaban kotu da aikata laifukan kutse da yin sata a filin jirgin sama
Source: UGC

Ta ce a yayin da ake gabatar da bincike, an gano cewa wanda ake zargi ya samu nasarar shiga cikin filin ajiye jirage da nufin satar muhimman abubuwa.

Yar sanda mai shigar da karar ta ce wannan laifin ya ci karo da sashe na 342 da 95 da ke a cikin kundin dokokin laifuka da hukuncin karya su.

Sai dai wanda ake zargi da aikata laifin, ya musanya wannan zargi da ake masa.

Mai shari'a Mr Taribo Jim, ya bada belin wanda ake zargin bisa sharadin gabatar da majibinta guda biyu, wadanda ya zamo tilas su kasance suna da aikin yi.

Jim ya ce majibintan zasu kasance mazauna yankin da kotun ta ke, kana ya daga sauraren karar har sai 9 ga watan Oktoba don ci gaba da shari'ar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel