Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari ya mayar da takardan takaransa hedkwatar APC

Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari ya mayar da takardan takaransa hedkwatar APC

Shugaba Muhammadu Buhari zai mayar da takardan takaransa hedkwatar APC dake unguwar Wuse, babban birnin tarayya Abuja.

Gamayyar Jami’an tsaro da ya kunshi rundunar DSS da na yan sanda sun kwace sakatariyar jam’iyyar domin tabbatar da tsaro gabanin zuwan shugaba Buhari.

Shugaba Buhari yayi dogon jawabi yayin wannan taro inda ya bukaci yan Najeriya da su zabeshi domin kada su mayar da Najeriya hannun wadanda suka dukufar da kasam daga shekarar 1999 zuwa 2015.

Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari ya mayar da takardan takaransa hedkwatar APC

Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari ya mayar da takardan takaransa hedkwatar APC
Source: Depositphotos

Yace: " A yau na gabatar da suna na ga jam'iyya ta APC domin neman takaran kujeran shugaban kasa a zaben bana."

Ina tabbatarwa mambobin jam'iyyar da yan Najeriya cewa idan aka zabe ni, zan cigaba da bauta muku har inda karfi na ya kare."

Kada mu sake mu yarda wadanda suka dukufar da kasa daga 1999 zuwa 2015 su mayar da mu gidan jiya."

A jiya Talata, shugaba Buhari ya karbi bakuncin yan kungiyar National Consolidation Ambassadors of Nigeria NCAN, wadanda suka siya masa takardan takarar zaben APC na kudi N45million.

Sun bayyana cewa babban dalilinsu na sayan masa wannan Fam shine domin karfafa masa guiwa wajen cigaba da ayyukan kwaran da yakeyi tun shekarar 2015 da yah au mulki.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel