Sayen Fam din takara na N45m ga shugaba Buhari ya sabawa doka - Ben Bruce

Sayen Fam din takara na N45m ga shugaba Buhari ya sabawa doka - Ben Bruce

Majalisar dattawa ta gargadi shugaban kasa Muhammadu Buhari akan yiwa doka da'a da ta shar'anta da kuma tanadi na hana bayar da duk wata gudunmuwa ta siyasa da ta haura N1m.

Kamar yadda shafin jaridar shafin jaridar ta The Punch ya ruwaito, majalisar ta kuma kausasa harshen ta dangane da yadda jam'iyyar APC ta sayar da fam dinta na bayyana kudirin takarar kujerar shugaban kasa kan zunzurutun kudi har na N45m.

Mataimakin shugaban kwamitin majalisar akan hulda da al'umma da kuma manema labarai, Ben Murray-Bruce, shine ya bayyana hakan yayin mayar da martani dangane da yadda wata kungiya ta sayawa shugaba Buhari fam din bayyana kudirin takara har na N45m wanda ya sabawa dokar zabe ta kasar nan.

Sanatan na jihar Bayelsa ya bayyana takaicin sa kwarai da aniyya dangane da yadda shugaba Buhari yayi rashin da'a ga dokar siyasa ta kasar nan da ta hana bayar da duk wata gudunmuwa ga 'yan siyasa da ta haura N1m.

Shugaba Buhari tare da fam din sa na bayyana kudiri

Shugaba Buhari tare da fam din sa na bayyana kudiri
Source: Depositphotos

Ya kuma bayyana yadda jam'iyyar APC ke hana ruwa gudu ta fuskar dakile kwarar romon dimokuradiyya sakamakon tsadar gaske da fam din ta na takarar kujerar shugaban kasa yayi, inda kowane dan takarar ta ya malalar da zunzurutun dukiya ta N45m yayin mallakar sa.

KARANTA KUMA: Gwamna Akeredolu zai kawo karshen rashin wutar lantarki na fiye da shekaru 10 a Kudancin jihar Ondo

Legit.ng ta ruwaito cewa, ko shakka ba bu wata kungiyar magoya bayan shugaba Buhari, ta saye fam din bayyana kudirin takarar kujerar shugaban kasa domin muradinta na ganin ya samu nasarar tazarce yayin zaben 2019.

Rahotanni sun bayyana cewa, an tsananta tsaro a ranar yau ta Laraba yayin da shugaba Buhari ya nufi shelkwatar jam'iyyar APC dake unguwar Wuse a babban birnin kasar nan na tarayya domin mayar da takardun sa na bayyana kudirin tsayawa takara.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel