EDO: Kungiyar malaman makaranta za su shiga yajin aikin sai baba ta gani a ranar Juma'a

EDO: Kungiyar malaman makaranta za su shiga yajin aikin sai baba ta gani a ranar Juma'a

- Kungiyar malamai ta kasa NUT reshen jihar Edo, zata fara yajin aikin sai baba ta gani daga ranar juma'a 14 ga watan Satumba

- Haka zalika, kungiyar ta bukaci gwamnati da ta maido da malaman da aka cire su daga aiki ba bisa ka'ida ba, da kuma karin albashi ga malaman firamare

- Sai dai shugaban hukumar SUBEB, Joan Oviawe, ya ce gwamnati na kokarin tattaunawa da malaman don gujewa shiga yajin aikin nasu

Sakamakon rashin cika alkawarin gwamnatin jihar Edo na biyawa malaman jihar bukatunsu, kungiyar malamai ta kasa (NUT) reshen jihar, ta ce zata fara yajin aikin sai baba ta gani daga ranar juma'a 14 ga watan Satumba.

A cikin wata takardar bayan taro da kungiyar ta saki a Benin, dauke da sa hannun Pius Okhueleigbe da Moni Itua, kungiyar ta ce: "Shuwagabannin zartaswa na kungiyar NUT na jihar Edo, tana cike da bacin rai, na gazawar gwamnatin jihar Edo na cika alkawuran da ta daukarwa malamai, duk da wa'adin kwanaki 21 da kungiyar ta bayar."

Bukatun da malaman suka gabatarwa gwamnatin jihar sun hada da baiwa malaman makarantun firamare da suka yi aiki a 2015 hakkokinsu wanda aka tabbatar a 2013, tare da kara masu albashi da kudaden hutu na watan Janairu zuwa Yuli.

KARANTA WANNAN: Cin hanci: Sama da N11bn aka kwato daga hannun jami'an rundunar yan sanda a shekaru 2

EDO: Kungiyar malaman makaranta za su shiga yajin aikin sai baba ta gani a ranar Juma'a

EDO: Kungiyar malaman makaranta za su shiga yajin aikin sai baba ta gani a ranar Juma'a
Source: Twitter

Haka zalika, kungiyar ta bukaci gwamnati da ta maido da malaman da aka cire su daga aiki ba bisa ka'ida ba, da kuma gyara tsarin wadanda aka hana karin matsayi, wanda hukumar ilimi bai daya ta jihar ta yi.

Sai dai shugaban hukumar ilimi bai daya ta jihar SUBEB, Joan Oviawe, ya ce gwamnati na kokarin tattaunawa da malaman don gujewa shiga yajin aikin nasu.

Kungiyar ta kuma buakci gwamnati da ta gaggauta fara daukar malamai aiki don cike gurbin malaman da suka ajiye aiki da wadanda suka mutu a makarantun firamare da sakandire kafin fara zangon karatu na gaba.

Don haka ne ma ta bukaci daukacin al'uma da su matsawa gwamnatin lamba don ganin ta cikawa malamai bukatunsu don gujewa fara yajin aikin sai baba ta gani, wanda a cewar kungiyar zai gurguntar da fannin ilimi a jihar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel