Buratai ya mayar da hedkwatar rundunar sojoji zuwa Gudumbali

Buratai ya mayar da hedkwatar rundunar sojoji zuwa Gudumbali

- Shugaban hafsan soji, Tukur Buratai ya mayar da hedkwatar rundunar sojoji zuwa Gudumbali

- Hakan na daga cikin matakin hukumar sojin na kokarin ganin ta kawo karshen ta'addanci a yanki arewa maso gabas

- Gudumbali na daga cikin garin da yan ta'addan Boko Haram suka kai hare-hare a baya-bayan nan a jihar Borno

Bayan dakile sabbin hare-hare da yan ta’addan Boko Haram suka kaiwa sansanonin sojoji a kokarinsu na daukar mataki kan yan ta’addan, shugaban hafsan soji, Laftanal Janar Tukur Buratai ya mayar da hedkwatar aiki na rundunar soji zuwa Gudumbali dakje karamar hukumar Guzamala dake jihar Borno, jaridar Vanguard ta ruwaito.

Ku tuna cewa Gudumbali, na daya daga cikin garuruwan da yan a’addan suka kai mamaya a makon da ya gabata dauke da motocin bindiga sannan sukayi ta harbi a sansanin soji, inda sojoji suka yi nasarar dakile harin tare da hana yunkurin yan ta’addan na kwace garin.

Buratai ya mayar da hedkwatar rundunar sojoji zuwa Gudumbali

Buratai ya mayar da hedkwatar rundunar sojoji zuwa Gudumbali
Source: Depositphotos

Don haka majiyar mu ta tattaro cewa domin kawo karshen hare-haren yan ta’addan a Arewa maso gabas, babban hafsan sojin ya mayar da hedkwatar rundunar zuwa Gudumbali a jihar Borno.

KU KARANTA KUMA: Buhari zai mayar da fam dinsa na takara a yau

Wata majiya tace shugaban sojin wadda ke kokarin ganin ya samu bayanin abubuwan dake faruwa kai tsaye a ayyukan sojin zaiziyarci dukkanin sansanin soji sannan ya gana da akarun sojin banda kwamandojinsu domin sanin idan akwai matsaloli.

A cewar majiyar zuwan bazata shugaban hafsan sojin zai yi ba tare da nuna wani alamu na cewa yana nan tafe ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel