Cin hanci: Sama da N11bn aka kwato daga hannun jami'an rundunar yan sanda a shekaru 2

Cin hanci: Sama da N11bn aka kwato daga hannun jami'an rundunar yan sanda a shekaru 2

- Rundunar yan sanda ta ce ta kwato akalla N11.1m daga hannun jami'anta da suka karba daga hanu jama'a a matsayin cin hanci

- Rundunar ta ce an mayarwa jama'a kudadadensu, yayin da aka kori akalla jami'ai 10 bisa aikata karba cin hanci a cikin shekaru 2

- Runduna yan sanda ta kuma ce zata cafke duk wanda ya je akwatin zabe da kudi don siyen kuri'u a zabukan da ke gabatowa

Mataimakin Kwamishinan yan sanda da ke kula da jin korafe korafen jama'a na sashen (PCRRU), Abayomi Shogunle, ya bayyana yadda yan sanda suka kwato N11.1m daga hannun wasu jami'an yansanda da suka karba daga hannun jama'a a matsayin cin hanci.

Mr. Shogunle ya bayyana hakan a Osogbo a wanni taron wayar da kai da aka shiryawa jami'an rundunar yan sanda, a ci gaba da shirye shiryen fuskantar zaben gwamnan jihar da za'a gabatar a ranar 22 ga watan Satumba.

Ya ce an mayarwa jama'a kudadadensu, yayin da aka kori akalla jami'ai 10 bisa aikata karba cin hanci da sauran laifukan da suka shafi cin amanar aikin.

KARANTA WANNAN: Cutar Zazzabin cizon sauro da Gudawa ta salwantar da rayukan Mutane 12 a sansanin Gudun Hijira na jihar Benuwe

Cin hanci: Sama da N11bn aka kwato daga hannun jami'an rundunar yan sanda a shekaru 2

Cin hanci: Sama da N11bn aka kwato daga hannun jami'an rundunar yan sanda a shekaru 2
Source: Depositphotos

"Bisa aikata laifukan da suka kaucewa koyarwar aikin dan sansa, shuwagabannin rundunar ta kori jami'ai sama da 10 a tsakanin shekaru biyu." a cewar sa.

Premium Times ta ruwaito ta ruwaito wasu jami'an rundunar yan sanda da ke karbar cin hanci, wadanda aka hasko su a bidiyo a lokacin da suke karbar cin hanci daga hanun matukan motoci.

Mr. Shogunle ya kuma bukaci jami'an rundunar da su kauracewa aikata laifukan cin hanci da rashawa, yana mai cewa duk wanda aka kama zai fuskanci hukunci dai dai da laifinsa.

Da ya ke jawabi dangane da zabukan da ke gabatowa, Mr Shogunle ya bada tabbacin cewa shirye shirye sun yi nisa na ganin cewa an gudanar da sahihin zabe, wanda babu rikici ko tayar da hankula a ciki.

"Rundunar yan sanda zata cafke duk wanda ya je akwatin zabe da kudi don siyen kuri'u" a cewar sa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel