Gwamna Akeredolu zai kawo karshen rashin wutar lantarki na fiye da shekaru 10 a Kudancin jihar Ondo

Gwamna Akeredolu zai kawo karshen rashin wutar lantarki na fiye da shekaru 10 a Kudancin jihar Ondo

Kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito, a ranar Talatar da ta gabata ne gwamnan jihar Ondo, Oluwarotimi Akeredolu, ya gudanar da zaman sauran ra'ayoyin al'ummar yankin Kudancin jihar sa dangane da rashin wutar lantarki na fiye da tsawon shekaru 10 da suka shude.

An gudanar da wannan zama har kashi biyu domin kawo karshen wannan ukuba ta rashin wuta lantarki , inda aka gudanar da zaman farko a daki taro na Willians dake garin Igbokoda a karamar hukumar Ilaje.

Kazalika an gudanar da zaman na biyu zuwa garin Okitiputa, inda gwamnan ya gana da mazauna yankin da kuma masu rike da kwangiyar gyaran wutar lantarki a yankin.

Matasa, Mata da kuma shugabannin al'ummomi daban-daban sun tofa albarkacin bakin su tare da bayyana halin kaka-nika-yi da wanna lamari na rashin wutar lantarki ya jefa su ciki.

Ana ci gaba da rashin wutar lantarki na fiye da shekaru 10 a Kudancin jihar Ondo

Ana ci gaba da rashin wutar lantarki na fiye da shekaru 10 a Kudancin jihar Ondo
Source: Depositphotos

Shugaban kamfanin samar da wutar lantarkin reshen Neja Delta, Ife Oyedele, ya yabawa gwamnatin jihar da ta tarayya dangane da wannan hobbasa da yunkuri na gyaran wutar lantarki da zai kawo sauki cikin harkokin al'ummar yankin.

KARANTA KUMA: Cutar Zazzabin cizon sauro da Gudawa ta salwantar da rayukan Mutane 12 a sansanin Gudun Hijira na jihar Benuwe

Al'ummar wannan yanki sun kuma bayyana da na saninsu dangane da yadda gwamnatin baya ta shafe shekaru 8 ba tare da tsinana ma su wani abin zo a gani ba kan wannan lamari da zai ingantawa rayuwarsu kwarai da aniyya.

A yayin jawabansa, gwamna Akeredolu ya sha alwashin kawo karshen wannan lamari na rashin wutar lantarki da suka shafe tsawon shekaru su na fama.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel