Buhari zai mayar da fam dinsa na takara a yau

Buhari zai mayar da fam dinsa na takara a yau

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai mayar da fam din sa na neman takara

- Zai mayar da fam din ne a babban sakatariyar APC dake Abuja da misalin karfe 3:30 na rana

- Wata kungiyar magoya bayansa ce ta mallaka masa fam din

Rahotanni sun kawo cewa ana sanya ran Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai mayar da fam din sa na neman takarar kujerar shugaban kasa a zaben 2019 a yau, Laraba, 12 ga watan Satumba.

Zai mayar da fam din ne babban sakatariyar jam’iyyar Progressives Congress (APC) mai mulki dakke babban birnin tarayya, Abuja da misalign karfe 3:30 na rana.

A ranar Talata, 11 ga watan Satumba ne kungiyar Nigeria Consolidation Ambassador Network (NCAN), ta gabatawa da Buhari da fam din takaran wadda ta siya masa.

Buhari zai mayar da fam dinsa na takara a yau

Buhari zai mayar da fam dinsa na takara a yau
Source: Depositphotos

Kungiyar dai ta siyi fam din ne akan naira miliyan 45 kamar yadda jam’iyyar APC ta bukaci farashin fam din dan takaran kujerar shugaban kasa ya kasance.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Kungiyar matasan Arewa sun koka akan tsadar fam din takara na jam’iyyun siyasa a zaben 2019 mai zuwa.

KU KARANTA KUMA: Ministar Buhari ta shiga matsala a gida bayan an wargaza APC

Shugaban kungiyar, Yerima Shettima ya bayyana hakan yayinda yake jawabi ga manema labarai a ranar Talata, 11 ga watan Satumba a sakatariyar babban jam’iyyar adawa Peoples Democratic Party (PDP) na jihar Kaduna.

Yayi zargin cewa da gangan aka kulla makircin sanyawa fam din takara domin hana matasa neman kujerun mulki a zabe mai zuwa tunda bazasu iya tattara kudin da aka bukata ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel