Da duminsa: Shugaba Muhammadu Buhari ya jagoranci taron FEC a yau

Da duminsa: Shugaba Muhammadu Buhari ya jagoranci taron FEC a yau

Karo na farko bayan dawowarsa daga kasar Sin, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranci taron majalisar zantarwa tarayya a yau Laraba, 12 ga watan Satumba 2018 a fadar shugaban kasa da ke Aso Villa, Abuja.

Taron majalisar zantarwan na yau ya tattari dukkan ministoci har da wadanda ba'a saba gani ba irinsu kwamandan hukumar tsaron lafiyan hanyoyin Najeriya wato FRSC, Boboye Oyeyemi.

Da duminsa: Shugaba Muhammadu Buhari ya jagoranci taron FEC a yau

Da duminsa: Shugaba Muhammadu Buhari ya jagoranci taron FEC a yau
Source: Facebook

Daga cikin wadanda suka halarci taron majalisar a yau sune ministan labarai da al'adu, Lai Mohammed.; ministan ayyukan ruwa, Abubakar Bwari; mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo; da sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha.

Da duminsa: Shugaba Muhammadu Buhari ya jagoranci taron FEC a yau

Da duminsa: Shugaba Muhammadu Buhari ya jagoranci taron FEC a yau
Source: Depositphotos

Kana ministan shari'a kuma babban lauyan tarayya, Abubakar Malami; ministan kasafin kudi, Udo Udoma ministan sadarwa, Adebayo Shittu; ministan tsaro, MAnsur Dan Ali; da karamar ministan kasafin kudi, Zainab Ahmed Shamsuna.

Da duminsa: Shugaba Muhammadu Buhari ya jagoranci taron FEC a yau

Da duminsa: Shugaba Muhammadu Buhari ya jagoranci taron FEC a yau
Source: Facebook

Majalisar zantarwa tarayya ta kunshi dukkan ministocin gwamnati, manyan masu baiwa shugaban kasa shawara, masu magana da yawunsa, shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, shugaban ma’aikatan gwamnati, sakataren gwamnatin tarayya da kuma duk wani mai fada aji a fadar shugaban kasa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu alabaranhausa@corp.legit.ng Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel