Zaben 2019: Matasan Arewa sun koka akan tsadar fam din takara

Zaben 2019: Matasan Arewa sun koka akan tsadar fam din takara

Kungiyar matasan Arewa sun koka akan tsadar fam din takara na jam’iyyun siyasa a zaben 2019 mai zuwa.

Shugaban kungiyar, Yerima Shettima ya bayyana hakan yayinda yake jawabi ga manema labarai a ranar Talata, 11 ga watan Satumba a sakatariyar babban jam’iyyar adawa Peoples Democratic Party (PDP) na jihar Kaduna.

Yayi zargin cewa da gangan aka kulla makircin sanyawa fam din takara domin hana matasa neman kujerun mulki a zabe mai zuwa tunda bazasu iya tattara kudin da aka bukata ba.

Shettima wadda ke naman takarar dan majalisar wakilai a karkashin PDP yayi kira ga jam’iyyun siyasa da nemo mafita domin ba matasa damar da zasu iyan mallakar fam din takaran.

Zaben 2019: Matasan Arewa sun koka akan tsadar fam din takara

Zaben 2019: Matasan Arewa sun koka akan tsadar fam din takara
Source: Depositphotos

Ya fadama manema labarai bayan mayar da fam dinsa sakatariyar PDP cewa matakin tattalin arziki da tabarbarewar tsaro a kasar ya daga sosai.

Shugaban kungiyar, ya kuma bayya cewa kungiyar na aiki tare da kungiyar dattawan arewa domin neman dan takara daga yankin a zaben shugaban kasa na 2019.

KU KARANTA KUMA: Buhari ya caccaki majalisar dokoki bayan an kwato N769bn na kudaden sata

Ya kara da cewa akwai bukatar chanja gwamnatin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a zabe mai zuwa.

A cewar Shettima babu wani ci gaba a kasar tun da gwamnatin Shugaban Kasa Muhammadu Buhar ta hau mulki.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel