Ni dai ba dan siyasa mai rauni bane – Kwankwaso ya mayarwa Buhari martani

Ni dai ba dan siyasa mai rauni bane – Kwankwaso ya mayarwa Buhari martani

Tsohon gwamnan jihar Kano kuma dan takaran kujeran shugaban kasa, Rabiu Musa Kwankwaso, ya mayarwa shugaba Muhammadu Buhari martani kan jawabin da yayi cewa yan siyasan da suka sauya sheka daga jam’iyyar All Progressives Congress, APC maraunata ne.

Shugaba Buhari, a jiya Talata, yayin karban takardan takarar zaben 2019 na jam’iyyar APC da wasu matasa suka saya masa ya bayyana cewa mafi raunin yan jam’iyyar ne suka fita.

Amma Sanata Kwankwaso ya mayar da martani kan wannan jawabi ta mai magana da yawunsa, Hajiya Binta Sipikin, inda tace: “Ai da shugaban kasa ya fito fili saboda mu gana wa yake nufi.”

Ni dai ba dan siyasa mai rauni bane – Kwankwaso ya mayarwa Buhari martani

Ni dai ba dan siyasa mai rauni bane – Kwankwaso ya mayarwa Buhari martani
Source: Twitter

“Amma na tabbata cewa Rabiu Kwankwaso da na sani ba mai rauni ba saboda nasarorin da ya samu na nan kowa ya gani.”

“Nasarorin da ya samu a shekaru hudu kacal a jihar Kano ya nuna cewa shugaba ne mai karfi, hagen nesa, da kuma tausayi wanda ya san abinda yake so kuma yadda zai samu.”

“Shi kadai ne shugaban da ya iya daura jihar Kano kan turba mai kyau da kuma gine-gine. Yayin sama da ayyuka 6000 tsakanin shekarar 2011 da 2015.. Mutum mai rauni ba zai iya wannan aiki ba.”

KU KARANTA: Ni da fina-finan Hausa, mutu ka raba -Jamila Nagudu

Sanata Rabiu Kwankwaso ya fita daga jam’iyyar APC ne tare da sauran abokan aikinsa a majalisar dattawa zuwa PDP. A yanzu, yana daga cikin yan takaran kujeran shugaban kasa 12 karkashin jam’iyyar PDP.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel