Yanzu Yanzu: 'Yan sanda sun damke lauyan Evans a kotu

Yanzu Yanzu: 'Yan sanda sun damke lauyan Evans a kotu

Mun samo daga Punch cewa wasu jami'an 'yan sanda sun kama wani lauya mai suna Olukoya Ogungbeje a babban kotun tarayya da ke Legas.

Ogungbeje yana daya daga cikin lauyoyin da suke kare gagararen hamshakin mai garkuwa da mutane Chukwudumeme Onwuamadike, wanda akafi sani da Evans.

An ce 'yan sandan da suka taho daga sashin binciken masu aikata manyan laifuka na jihar Legas (SCID), Panti, sunyi caraf da lauyan ne a lokacin da ya yi farkin din motarsa a harabar kotun tarayyar a safiyar yau

Yanzu Yanzu: 'Yan sanda sun damke lauyan Evans a kotu

Yanzu Yanzu: 'Yan sanda sun damke lauyan Evans a kotu
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Takarar Saraki a PDP na fuskantar tarnaki, ya ce ba zai janye ba

Ogungbeje ya zo kotun ne domin ya gurfana gaban mai Alkali Muslim Hassan amma sai gashi 'yan sandan sunyi awon gaba dashi.

Ku biyo mu domin samun karin bayani...

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel