Cutar Zazzabin cizon sauro da Gudawa ta salwantar da rayukan Mutane 12 a sansanin Gudun Hijira na jihar Benuwe

Cutar Zazzabin cizon sauro da Gudawa ta salwantar da rayukan Mutane 12 a sansanin Gudun Hijira na jihar Benuwe

A yayin da rikicin makiyaya ya jefa mutane da dama neman mafaka a sansanin gudun hijira dake jihar Benuwe, a halin yanzu annobar cututtukan zazzabin cizon sauro da Gudawa sun afka ma su inda rayukan mutane 12 suka salwanta cikin wata guda da ya gabata.

Kamar yadda shafin jaridar The Punch ya ruwaito, annobar wannan cututtuka ba ta takaita kadai akan manya ba domin kuwa har kananan yara sun kamu musamman cutar Gudawa gami da rashin koshin lafiya.

Rahotanni sun bayyana cewa, ma'aikatan kiwon lafiya tare da hadin gwiwar kungiyar bayar da agajin lafiya na gaggawa sun taikaita tasirin wannan annoba wanda da yanzu labari ya sha ban-ban.

Cutar Zazzabin cizon sauro da Gudawa ta salwantar da rayukan Mutane 12 a sansanin Gudun Hijira na jihar Benuwe

Cutar Zazzabin cizon sauro da Gudawa ta salwantar da rayukan Mutane 12 a sansanin Gudun Hijira na jihar Benuwe
Source: Depositphotos

Daya daga cikin mazauna sasanin, Ucha Ikpachi, wanda ya bayyana damuwarsa dangane da aukuwar wannan annoba da mace-macen rayuka a sansanin, ya kuma nemi gwamnatin tarayya akan ta kawo ma su agaji na saukaka wannan ukuba domin komawa mahallansu cikin gaggawa.

Ya ci gaba da cewa, gwamnatin jihar na iyaka bakin kokarin ta na kawo saukin ciki al'amurran su inda a halin yanzu lamarin ya ci tura da sai gwamnatin tarayya ta agaza da na ta tallafin.

KARANTA KUMA: Hukumar INEC ta yi barazanar dakatar da zaben 2019 kan rikita-rikitar Siyasa

Kazalika, shugaban cibiyar bayar da agajin gaggawa reshen jihar, Emmanuel Shior, ya tabbatar da aukuwar wannan annoba a sansanin na 'yan gudun hijira, inda ya sake jaddada yadda lamarin ya ci tura baya ga tallafin gwamnatin jihar.

Legit.ng ta fahimci cewa, akwai kimanin mutane 400, 000 dake fake a sansanan gudun hijira musamman a yankin Arewa ta Gabas da ta'addancin Boko Haram ya haramta ma su zama a muhallansu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel