Bani da matsala da Gwamna Abubakar - Oshiomhole

Bani da matsala da Gwamna Abubakar - Oshiomhole

- Shugaban jam'iyyar APC na kasa Adams Oshiomhole yace ba da matsala da gwamnan jihar Bauchi

- Oshiomhole yace damuwar si shine yadda jam'iyyar zata yi nasara a zabe musamman na shugaban kasa

- Gwamna Abubakar dai ya ziyarci shugaban jam'iyyar ne a gidansa dake Abuja

Adams Oshiomhole, shugaban jam’iyyar All Progressive Congress (APC) ya bayyana cewa bashi da kowani matsala da Gwamna MA Abubakar na jihar Bauchi.

Ya bayar da tabbacin hakan a lokacin da ya karbi bakuncin gwamnan a gidansa dake Abuja a ranar Talata, 11 ga watan Satumba.

Yace babban damuwarsa shine nasarar jam’iyyar a dukkanin matakai a zabe mai zuwa.

Bani da matsala da Gwamna Abubakar - Oshiomhole

Bani da matsala da Gwamna Abubakar - Oshiomhole
Source: Depositphotos

Duba kai tsaye ga ziyarar gwamnan “Bani da matsala da kai, mai girma gwamna. Damuwana shinenasarar zabe musamman na shugaban kasa muna so mu sake nasara a wasu jihohin annan mu sau Karin yan majalisa. Nayi imani da kai.”

Sannan yayiwa bakin nasa fatan komawa gida lafiya.

Da yake Magana a nashi bangaren, Gwana Abubakar ya bayyanawa mai masaukin bakin nasa cewa yazo gidansa ne domin sanar dashi batun mayar da fam dinsa na takara a sakatariyaar jam’iyyar na kasa.

KU KARANTA KUMA: Buhari ya caccaki majalisar dokoki bayan an kwato N769bn na kudaden sata

Gwamnan ya samu rakiyan mambobin majalisun dokoki na kasa da jiha, mambobin kwamiti da manyan masu ruwa da tsaki na jam’iyyar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel