2019: Ba mu amince da sulhu ba - Gwamnonin PDP

2019: Ba mu amince da sulhu ba - Gwamnonin PDP

- Kungiyar gwamnonin jam'iyyar PDP ta ki amince da yin sulhu wajen fitar da dan takarar shugabancin kasa a jam'iyyar

- Kwamitin amintattu na jam'iyyar da masu ruwa da tsaki ne suka bayar da shawarar yin sulhun

- Gwamnonin sun ce idan ana son yin adalci ya zama dole ayi zaben fitar da gwamni domin kowa halinsa ta kwace shi

A jiya, Talata ne gwamonin jam'iyyar PDP suka nuna kin amincewarsu da kirar da kwamitin amintattu na jam'iyyar tayi na zaban dan takarar shugabancin kasa a jam'iyyar ba tare da gudanar da zaben fidda gwani ba.

Gwamnonin kuma sun yanke shawarar cewa za'a gudanar da babban taron jam'iyyar na kasa ne a Fatakwal ta jihar Rivers inda za'a gudanar da zaben fidda gwamni domin fitar da dan takarar shugabanin kasa.

2019: Ba mu amince da sulhu ba - Gwamnonin PDP

2019: Ba mu amince da sulhu ba - Gwamnonin PDP
Source: Depositphotos

DUBA WANNAN: Takarar Saraki a PDP na fuskantar tarnaki, ya ce ba zai janye ba

Idan ba'a manta ba, gwamnonin sun fitar da wata sako a ranar Litinin inda su kayi bukaci a kira taro na dukkan masu neman tikitin takarar jam'iyyar, Ciyaman din jam'iyyar, shugabanin jam'iyya na kasa biyu da kuma shugabanin jam'iyyar daga majalisar tarayya.

Wani majiya ta ya hallarci taron da su kayi jiya ya ce gwamnonin sun yanke shawarar cewa zaben fidda gwani shine kawai hanyar da za'ayi domin yin adalci ga duka 'yan takarar.

"Gwamnonin sun ki amincewa da sulhu wajen fitar da dan takarar shugabancin kasa. Sun ce dukkan 'yan takarar su gwabza a zaben fitar da gwamni ta yadda kowa halinsa ta kwace shi. Suna son wanda ya fi cancanta ya zama dan takarar jam'iyyar," inji majiyar.

A kan batun garin da za'a gudanar da taron kasa na jam'iyyat, majiyar ta ce an ambaci jihohin Enugu, Akwa Ibom da Rivers amma gwamnonin sun zabi jihar Rivers saboda tafi sauran jihohin wuraren sauke baki.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel