Hukumar INEC ta yi barazanar dakatar da zaben 2019 kan rikita-rikitar Siyasa

Hukumar INEC ta yi barazanar dakatar da zaben 2019 kan rikita-rikitar Siyasa

Hukumar zabe ta kasa watau INEC, ta yi gargadi gami da barazanar dakatar da kuma ɗage gudanar da babban zabe na 2019 a sakamon rikice-rikicen siyasa dake faman aukuwa a kasar nan a sanadiyar hankoron madafan iko daga bangaren 'yan siyasa.

Shugaban hukumar, Farfesa Mahmoud Yakubu, shine ya bayyana wannan damuwa da cewar muddin lamarin siyasa ya ci gaba da sanadin aukuwar rikici a kasar nan to kuwa ba bu shakka zaben 2019 ba zai gudana ba kamar yadda aka tsara.

Kamar yadda shafin jaridar Leadership ya ruwaito, shugaban hukumar ya bayyana damuwarsa ne a sakamakon yadda 'yan siyasa ke faman barazanar zubar da jinin al'umma cikin wasu faifaye na bidiyo yayin yakin su na neman zabe.

Shugaban Hukumar INEC; Farfesa Mahmoud Yakubu

Shugaban Hukumar INEC; Farfesa Mahmoud Yakubu
Source: Depositphotos

Farfesa Yakubu ya bayyana hakan ne yayin ganawar sa da wani jigo na hukumar mai ruwa da tsaki kan harkokin zaben gwamnan jihar Osun da zai wakana cikin wannan wata na Satumba.

Yake cewa, lamari na siyasa a kasar nan na neman sanadiyar abinda zai dakatar da zaben 2019, inda yake kira akan su shiga taitayinsu tare da kauracewa wannan mummunan yanayi da ke barazana gami da zagon kasa ga zaman lafiyar al'umma da kasa baki daya.

KARANTA KUMA: Hadimin Gwamnan Jihar Filato ya yi gamo da ajali a Kasar India

A yayin ci gaba da gargadi da kuma fadakar da 'yan siyasar masu hankoron madafan iko ta kowane hali, shugaban hukumar ya kuma bayyana cewa ba bu yadda za a yi zabe ya gudana a kasar nan matukar ba bu zaman lafiya da kwanciyar hankali a cikin ta

Jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, shugaban kasa Muhammadu Buhari zai shilla kasar Amurka tare da tawagarsa domin halatar taron majalisar dinkin duniya karo na 73 da za a gudanar a ranar 18 ga watan Satumba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel