Da duminsa: Zan kawo kaina ofishinku ranan 16 ga watan Oktoba – Fayose ga EFCC

Da duminsa: Zan kawo kaina ofishinku ranan 16 ga watan Oktoba – Fayose ga EFCC

- Yana sauka daga mulki, Fayose zai bayyana gaban EFCC

- Ya ce a matsayinsa na dan Najeriya mai mutunci da kima, ya kamata a mika kansa

- Zai kare wa'adinsa matsayin gwamnan jihar Ekiti ranan 16 ga wtaan Oktoba

Gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose, ya rubutawa hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa wato EFCC wasika domin sanar da su cewa zai gabatar da kansa a ranan Talata, 16 ga watan Oktoba, 2018.

A wata wasika da ya sanya hannu da kansa, ya ce yana sanar da hukumar da niyyar bayyana gabansu domin amsa tambayoyi kan zargi da tuhume-tuhumen da hukumar ke masa.

Wannan wasika da ya rubuta ranan 10 ga watan Satumba, ya ce dalilin mika wasikan shine kan wasu take-take da hukumar keyi a kwanakin bayan nan na daskarar da asusun bankinsa da kokarin kwace masa dukiyoyinsa.

KU KARANTA: Ministar Buhari ta shiga matsala a gida bayan an wargaza APC

Yace: “Nuna bukatar hukumar na inyi bayani kan wasu abubuwa amma suka kasa saboda kariyan da kundin tsarin mulkin Najeriya a matsayin gwamnan jihar Ekiti.”

Gwamna Fayose wanda ya kasance cikin rikici da hukumar yaki da rashawan kuma ya kasance cikin kotu da hukumar kan dukiyar jihar da nasa.

Wa’adin gwamna Fayose zai kare ranan 16 ga watan Oktoba inda zai mika ragamar mulki ga Kayode Fayemi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel