Ministar Buhari ta shiga matsala a gida bayan an wargaza APC

Ministar Buhari ta shiga matsala a gida bayan an wargaza APC

- Kai ya rabu a jam'iyyar APC reshen jihar Taraba bayan an wargaza shugabannin jam'iyyar

- Hasashe sun nuna ministar Buhari, Aisha Alhassan ta shiga tsaka mai wuya

- Dama dai shugabannin jam’iyyar na kasa na kokwanto akan duk wani motsi nata tun bayan da ta nuna yin Atiku sama da Buhari

An samu rabuwar kai a tsakanin mambobin APC a jihar Taraba kan rantsar da sabon shugaba da sauran jagororin jam’iyyar a jihar da shugaban jam’iyyar na kasa, Adams Oshiomhole yayi a Abuja.

A ranar Litinin, 10 ga watan Satumba Oshiomhone ya rantsar da Hon. Ibrahim Tukur El-Sudi a matayin shugaban APC a jihar Taraba sannan ya bukaci day a tabbatar da mambobi da masu ruwa da tsaki sun aiki don nasarar jam’iyyar.

El-Sudi ya maye gurbin Abdulmumini Vaki, wadda ya zamo shugaban jam’iyyar a watan Yuni, tare da cikakken goyon bayan ministar harkokin mata, Misis Aisha Jummai Alhassan.

Malam Garba Daauda, wani mamban jam’iyyar kuma na kusa da Misis Alhassan, yace matakin sakatriyar APC na kasa zai kara kawo rudani a jam’iyyar a jihar Taraba.

Yace ba daidai bane rantsar da wani mutun a matsayin shugaba yayinda wni daban wadda aka zaba ke kan wannan matsayi.

Ministar Buhari ta shiga matsala a gida bayan an wargaza APC

Ministar Buhari ta shiga matsala a gida bayan an wargaza APC
Source: Facebook

Sai dai Mista Aaron Artimas, sabon kakakin jam’iyyar da aka rantsar tare da sabbin jami’anta, ya bayyana cew sun samu goyon bayan kaso 80 na mambobin jam’iyyar a jihar.

Yace sabon jagora na da tsakanin yan takaran kujerar gwamna 13 zuwa 14 tare da masu ruwa datsakin siyasa na Taraba yayinda tsohon jagora karkashin Vaki ke tafiyar da kimanin kaso 20 na mambobin jam’iyyar.

KU KARANTA KUMA: Yan Najeriya zasu dunga samun wutar lantarki na sa’o’i 24 idan suka sake zabar Buhari – Amaechi

Sai dai ba’a samu jin ta bakin Maman Taraba da tsohon shugaban jam’iyyar ba yayinda aka ce suna Abuja suna gaanawa.

Majiyoyi sun bayyana cewa Mama Taraba ce ke daukar nauyin lamuran APC a jihar ita kadai, amma furucinta a shekarar bara da ta nuna fifiko akan tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar yasa shugabannin jam’iyyar na kasa na kokwanto akan duk wani motsi nata.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel