Yan Najeriya zasu dunga samun wutar lantarki na sa’o’i 24 idan suka sake zabar Buhari – Amaechi

Yan Najeriya zasu dunga samun wutar lantarki na sa’o’i 24 idan suka sake zabar Buhari – Amaechi

- Ministan sufuri ya shawarci yan Najeriya da su sake zabar Shugaba Buhari idan har suna son jin dadin wutar lantarki na sa'o'i 24

- Amaechi ya zayyano tarin nasarorin da gwamnatin APC ta samu

- Yace sunyi nasarar magance matsalar tsaro, yaki da cin hanci da rashawa, gyara hanyoyi da sauransu

- Ya jadadda cewa Shugaban kasa mai ci ya cancanci yan Najeriya su sake zabarsa

Ministan sufuri Rotimi Amaechi yace yan Najeriya zasu dunga samun wutar lantarki tsawon sa’o’i 24 idan har suka sake zabar Shugaban Kasa Muhammadu Buhari.

Yace gwamnatin Buhari ta samu nasarori da dama a tsaro, hanya, yaki da cin hanci da rashawa da dai sauransu.

Ministan wadda yayi Magana a jiya a taron manema labarai yace gwamnatin na magance kashe-kashe dake da alaka da makiyaya.

Yan Najeriya zasu dunga samun wuta a sa’o’i 24 idan suka sake zabar Buhari – Amaechi

Yan Najeriya zasu dunga samun wuta a sa’o’i 24 idan suka sake zabar Buhari – Amaechi
Source: Depositphotos

Amaechi yace yan Najeriya sun koya masa wani darasi a siyasa cewa shiyasa yanzu komai baya damunsa. Domin a cewarsa mutanen da suka yi maka wakar yabo a yau su din ne zasu yi maka wakar suka a gobe.

KU KARANTA KUMA: APC tace babu wanda zai nemi takarar kujerar Shugaban kasa da Buhari

Yace sun taka muhimmin rawar gani ta fannin sufuri. Ya kara da cewa sun kashe kudin al’umma wajen yin ayyuka da farfado da tattalin arzikin kasar don haka Shugaba Buhari ya cancanci a sake zabarsa.

Yace ayyuka da dama da gwamnatin tayi ya isa shaida, sannan cewa fannin wutar lantarki ya inganta kuma ana aiki a kai don ganin an samu yalwataccen wuta a fadin kasar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel