APC tace babu wanda zai nemi takarar kujerar Shugaban kasa da Buhari

APC tace babu wanda zai nemi takarar kujerar Shugaban kasa da Buhari

Mun ji cewa Sakataren Jam’iyyar APC na kasa Alhaji Mai Mala Buni ya nuna cewa Jam’iyyar APC mai mulki ta amincewa Shugaba Buhari ya cigaba da rike mata tuta a zabe mai zuwa na 2019.

APC tace babu wanda zai nemi takarar kujerar Shugaban kasa da Buhari

Babu wanda zai ja da Buhari a APC inji Sakataren Jam'iyya
Source: UGC

Alhaji Mai Mala Buni ya tabbatar da cewa Majalisar zartarwa watau NEC ta Jam’iyyar APC ta amince da cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya sake yin takarar Shugaban kasa a zaben 2019 ba tare da wani yayi masa hamayya a APC ba.

Alhaji Buni ya bayyana cewa Majalisar NEC ita ce koli a Jam’iyyar APC kuma ta dauki matakin cewa babu wanda zai nemi ya kara da Buhari. Sakataren Jam’iyyar yace NEC tayi itiffakin cewa Buhari ne zai rikewa APC tuta a 2019.

KU KARANTA: Gwamnatin Buhari ta ba barayi wurin labewa - Frank

Sakataren Jam’iyyar yace idan har Majalisar ta NEC ta yi na’am da mataki yana nufin cewa daukacin ‘Ya ‘yan Jam’iyyar na goyon bayan haka. Buni yace har a irin kasashen wajen da aka cigaba, ana daukar irin wadannan mataki.

APC tace ba za ta hana kowa takarar kujerar Shugaban kasar ba amma dai Buhari ne a kan gaba kuma sai yadda yayi. Kwanaki APC ta amince da cewa za ayi amfani da tsarin kato-bayan-kato ne wajen zaben ‘Dan takarar Shugaban kasa.

Kun samu labari cewa Rotimi Amaechi ya bayyana cewa karo-karo aka yi wajen sayawa Shugaba Muhammadu Buhari fam din sake takarar Shugaban kasa a Jam’iyyar APC a zaben 2019 na badi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit

Mailfire view pixel