Zaben 2019: Masana tattalin arziki daga Landan sun yi hasashen faduwar Shugaba Buhari

Zaben 2019: Masana tattalin arziki daga Landan sun yi hasashen faduwar Shugaba Buhari

- Masana tattalin arziki daga Landan sun yi hasashen faduwar Shugaba Buhari

- Sun ce jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP) ce zata lashe zaben

- Sun zayyana tabarbarewar tattalin arziki da kuma tsadar rayuwa a matsayin dalilai

Bangaren masana tattalin arzikin kasa watau Economist Intelligence Unit (EIU) na wata mujallar birnin Landan watau The Economist Magazine ta yi hasashen faduwar Shugaba Buhari zaben 2019 da za'a gudanar.

Zaben 2019: Masana tattalin arziki daga Landan sun yi hasashen faduwar Shugaba Buhari

Zaben 2019: Masana tattalin arziki daga Landan sun yi hasashen faduwar Shugaba Buhari
Source: Facebook

KU KARANTA: Sojin Najeriya sun yi raga-raga da 'yan Boko Haram

Mujallar dai wadda ake bugawa a birnin na Landan haka zalika tayi hasashen cewa jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP) ce zata lashe zaben da za'a gudanar nan da 'yan watanni kadan.

Legit.ng ta samu cewa masanan sun zayyana dalilan da suka hada da tabarbarewar tattalin arziki da kuma tsadar rayuwa a matsayin abubuwan da za su sa al'ummar kasar su iya juyawa Shugaba Buhari baya a yayin zaben.

A wani labarin kuma, Mun samu labarin cewa an tashi ba'a cimma matsaya ba a wani zaman sasanci da aka so yiwa 'yan takarar shugaban kasar Najeriya a karkashin inuwar jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) da wasu jiga-jigan jam'iyyar.

Kamar dai yadda muka samu, taron wanda aka gudanar a ofishin uwar jam'iyyar a garin Abuja ya samu halartar shugaban jam'iyyar ta PDP Cif Uche Secondus, gwamnonin jam'iyyar ta PDP da sauran jiga-jigan jam'iyyar.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel