Shugaba Buhari zai sake shillawa ya bar Najeriya zuwa kasar Amurka

Shugaba Buhari zai sake shillawa ya bar Najeriya zuwa kasar Amurka

- Shugaba Buhari zai sake shillawa ya bar Najeriya zuwa kasar Amurka

- Shugaba Buhari zai yi magana a wajen taron majalisar dinkin duniya

- Taron na karo na 73 da za'a gudanar da shi ne a garin New York na kasar Amurka

Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ana sa ran zai jagoranci tawagar 'yan Najeriya zuwa taron majalisar dinkin duniya karo na 73 da za'a gudanar a garin New York na kasar Amurka nan ba da dadewa ba.

Shugaba Buhari zai sake shillawa ya bar Najeriya zuwa kasar Amurka

Shugaba Buhari zai sake shillawa ya bar Najeriya zuwa kasar Amurka
Source: Depositphotos

KU KARANTA: Gwamnatin Buhari tamkar mafaka ce ga barayin Najeriya

Kamar yadda muka samu, ministan harkokin waje na Najeriya Mista Geoffrey Onyeama shine ya sanar da hakan ga manema labarai a garin Abuja ranar Talatar da ta gabata inda kuma yace taron za'a gudanar da shi ne a ranar 18 ga watan Satumbar da muke ciki.

Legit.ng haka zalika ta samu daga wajen ministan na harkokin waje cewa shugaban kasar zai yi magana a wajen taron da zai samu halartar shugabannin duniya inda ake sa ran zai ilmantar da su.

A wani labarin kuma, Bangaren masana tattalin arzikin kasa watau Economist Intelligence Unit (EIU) na wata mujallar birnin Landan watau The Economist Magazine ta yi hasashen faduwar Shugaba Buhari zaben 2019 da za'a gudanar.

Mujallar dai wadda ake bugawa a birnin na Landan haka zalika tayi hasashen cewa jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP) ce zata lashe zaben da za'a gudanar nan da 'yan watanni kadan.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel