Gyaran taku: Jam'iyyar PDP ta sake sanya ranakun gudanar da zabukan fitar da gwanin ta

Gyaran taku: Jam'iyyar PDP ta sake sanya ranakun gudanar da zabukan fitar da gwanin ta

- Jam'iyyar PDP ta sake sanya ranakun gudanar da zabukan fitar da gwanin ta

- Tayi haka ne saboda wadanda ka iya dawowa jam'iyyar daga APC

- Wannan dai duk dubarun siyasa ne

Babbar jam'iyyar adawa a Najeriya ta Peoples Democratic Party (PDP) ta sanar da wasu 'yan canje-canje game da ranakun gudanar da zabukan fitar da gwanin ta a dukkan matakan mulkin da zai bayar da damar shiga zabukan 2019.

Gyaran taku: Jam'iyyar PDP ta sake sanya ranakun gudanar da zabukan fitar da gwanin ta

Gyaran taku: Jam'iyyar PDP ta sake sanya ranakun gudanar da zabukan fitar da gwanin ta
Source: Depositphotos

KU KARANTA: Ana zargin cif Bola Tinubu da badakalar Naira biliyan 160

Wannan dai kamar yadda muka samu, jam'iyyar tayi hakan ne domin ta baiwa wadanda aka bata ma rai daga jam'iyyar APC mai mulki damar su dawo jam'iyyar ta su kuma har ma a dama da su.

Legit.ng ta samu cewa haka zalika ma jam'iyyar ta Peoples Democratic Party (PDP) ta kara wa'adin sayar da fom din takarar ga dukkan masu sha'awa da kwanaki bakwai.

Yanzu dai kamar yadda muka samu, 15 ga watan Satimba ne za'a gudanar da zabukan fitar da gwanin 'yan majalisar jiha, na majalisar tarayya kuma za'a yi shi 30 ga watan Satumba.

Sai kuma na Sanatoci za'a yi shi ne a ranar 28 ga wata yayin da kuma na gwamnoni za'a yi shi ne shima a ranar 28 ga wata.

A wani labarin kuma, Mun samu labarin cewa an tashi ba'a cimma matsaya ba a wani zaman sasanci da aka so yiwa 'yan takarar shugaban kasar Najeriya a karkashin inuwar jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) da wasu jiga-jigan jam'iyyar.

Kamar dai yadda muka samu, taron wanda aka gudanar a ofishin uwar jam'iyyar a garin Abuja ya samu halartar shugaban jam'iyyar ta PDP Cif Uche Secondus, gwamnonin jam'iyyar ta PDP da sauran jiga-jigan jam'iyyar.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel