Gwamnonin Jam’iyyar PDP na zargin Buhari da kokarin hana ayi zaben kirki a 2019

Gwamnonin Jam’iyyar PDP na zargin Buhari da kokarin hana ayi zaben kirki a 2019

Mun samu labari cewa Gwamnonin Jam'iyyar PDP sun yi kaca-kaca da Shugaban kasa Muhammadu Buhari na kin amincewa da gyarar da Majalisar Tarayya tayi wa dokar zaben kasa.

Gwamnonin Jam’iyyar PDP na zargin Buhari da kokarin hana ayi zaben kirki a 2019

Gwamnonin Jam’iyyar PDP wajen wani taro kwanakin baya
Source: Depositphotos

Kwanaki ne Shugaba Buhari ya ki amincewa da kudirin da Majalisa ta kawo masa na gyara dokar zabe. Hakan ta sa wasu su ka fara cewa Shugaban na gudun ayi amfani da na’u’rorin zamani a zaben 2019 wanda yayi maza ya karyata.

Gwamonin Jam’iyyar adawa na PDP sun yi tir da wannan mataki da Shugaban kasar ya dauka. Shugaban Gwamnonin PDP na kasa Ayodele Fayose ya fitar da jawabi a farkon makon nan inda yace Gwamnati na tsoron ayi zaben kwarai.

KU KARANTA:

Gwamnan na Ekiti ya kara nanata cewa Shugaba Buhari na gudun ayi amfani da na’urorin zamani a zabe mai zuwa. Bayan nan kuma Ayo Fayose ya soki yadda ake murde zabukan Kasar kamar yadda ya wakana a Ribas, Osun da Jihar Ekiti.

Har wa yau, Gwamnonin Jihohin sun yi Allah-wadai da abin da ‘Yan Sandan Najeriya su ka yi wa wani Dattijon Kasar Edwin Clark inda aka bincike masa gida a Abuja babu gaira babu dalili. Jama’a da dama dai sun soki wannan abu da ya faru tuni.

Kwanaki dai idan ba ku manta ba Shugaba Buhari yayi karin haske game da dokar yi wa tsarin zabe garambawul da ya ki sa wa hannu inda yace sam ba ya gudun ayi amfani da na’u’rorin zamani a 2019 domin shi ya ga amfanin su a zaben 2015.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel