Ba a sabawa dokar kasa wajen sayawa Buhari fam ba - Buhari Campaign Organisation

Ba a sabawa dokar kasa wajen sayawa Buhari fam ba - Buhari Campaign Organisation

Ministan sufurin Najeriya watau Rotimi Amaechi ya bayyana cewa karo-karo aka yi wajen sayawa Shugaba Muhammadu Buhari fam din sake takarar Shugaban kasa a Jam’iyyar APC a zaben 2019.

Ba a sabawa dokar kasa wajen sayawa Buhari fam ba - Buhari Campaign Organisation

Jama'a sun hadu sun sayawa Buhari fam din takara
Source: Depositphotos

Rotimi Amaechi wanda shi ne Shugaban yakin neman zaben Buhari yayi karin haske game da yadda aka hadawa Shugaban kasar kudin fam din takara. Amaechi wasu ne da ke son ganin cigaban Najeriya su ka sayawa Buhari fam kwanaki.

Darektan na Buhari Campaign Organisation ya bayyanawa ‘Yan jarida cewa ba a sabawa wata doka wajen sayen wannan fam ba domin kuwa Bayin Allah ne su ka hada karfi su ka bada abin da su ke da shi daidai gwargwadon karfin aljihun su.

KU KARANTA: Obasanjo na neman a halatta tabar wiwi a Afrika

Minista Rotimi Amaechi yace wasu sun kawo N50, 000 yayin da wasu kuma su ka bada kusan Miliyan 1 wajen ganin an sayawa Buhari fam din takarar. Ministan yace mutane da yawa ne su ka hada kudin ba wai mutum daya ko biyu ba.

Wata kungiyar “Nigeria Consolidation Ambassador Network” watau NCAN ce ta saya Buhari fam domin ya nemi tazarce. Dokar kasa dai tace bai halatta ‘Yan takara su karbi gudumuwar da ta haura Naira Miliyan 1 daga mutum guda ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel