Abinda ya sanya na sauya sheka tare da Kwankwaso zuwa jam'iyyar APC - Sanata Bello

Abinda ya sanya na sauya sheka tare da Kwankwaso zuwa jam'iyyar APC - Sanata Bello

Da sanadin shafin jaridar The Nation mun samu rahoton cewa, wani tsohon Sanatan jihar Kano, Muhammad Bello, a ranar Talatar da ta gabata ya bayyana dalilin sa na sauya sheka zuwa jam'iyyar APC tare tsohon gwamnan jihar, Mallam Ibrahim Shekarau.

Tsohon Sanatan Kano ta Tsakiya dai ya bayyana cewa, ya sauya shekarsa ta siyasa ne bisa ga jagorancin Shekarau domin karfafa ikon jam'iyyar wajen tabbatar da nasarar shugaban kasa Muhammadu Buhari da kuma gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje a zaben 2019.

Legit.ng ta ruwaito cewa, a yayin da jam'iyyar PDP ta kasa ta rusa shugabancin ta dake reshen jihar Kano, ya sanya tsohon gwamnan ya sauya sheka tare da raba gari da ita a karshen makon da ya gabata.

Sai dai ko shakka babu wasu daga cikin 'yan gani kashenin na Shekarau da suka hadar har da Sanata Bello sun yanke shawarar tafiya tare da Ubangidansu yayin da wasu suka raba gari da shi ta sake gyara zamansu cikin jam'iyyar ta PDP.

Abinda ya sanya na sauya sheka tare da Kwankwaso zuwa jam'iyyar APC - Sanata Bello

Abinda ya sanya na sauya sheka tare da Kwankwaso zuwa jam'iyyar APC - Sanata Bello
Source: Depositphotos

A yayin ganawar sa da manema labarai bayan karbar katinsa na jam'iyya a mazabarsa dake unguwar Fagge cikin karamar hukumar ta Fagge, Sanata Bello ya bayyana cewa a halin yanzu ba ya da wani ra'ayi na takarar kowace kujera karkashin sabuwar jam'iyyar ta sa ta APC.

KARANTA KUMA: Za mu ci gaba da tatse dukiyar al'umma a hannun barayin gwamnati - Buhari

Sai dai a nasa bangaren, Sanata Bello ya bayyana cewa ya yanke wannan shawara ne ta sauya sheka zuwa APC domin karfafa ta wajen tabbatar da nasararta a matakai da kujerun siyasa daban-daban yayin babban zabe na 2019.

Sanata Bello wanda tsohon kwamishina ne a yayin gwamnatin Mallam Shekarau ya yi bugun gaba tare da cika baki da cewar goyon bayansa zuwa ga jam'iyyar kadai ya isa ya tabbatar da nasarorin ta a fadin jihar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel