Shugabannin Kananan Hukumomin Legas da manyan APC sun yi wa ‘Dan takarar Tinubu mubaya’a wajen tika Ambode da kasa

Shugabannin Kananan Hukumomin Legas da manyan APC sun yi wa ‘Dan takarar Tinubu mubaya’a wajen tika Ambode da kasa

A halin yanzu Gwamnan Jihar Legas Akinwunmi Ambode yana cikin wani mawuyacin hali wajen shirin sa na zarcewa a kan karagar mulki bayan da babban Jigon siyasar Kasar Yarbawa Bola Tinubu ya juya masa baya.

Shugabannin Kananan Hukumomin Legas da manyan APC sun yi wa ‘Dan takarar Tinubu mubaya’a wajen tika Ambode da kasa

Shugabannin APC da wasu manya na neman hana Ambode motsi a APC
Source: Depositphotos

Ana kishin-kishin din cewa tsohon Gwamnan Legas Asiwaju Bola Tinubu yayi fatali da Ambode inda yake yunkurin kakaba Jide Sanwo-Olu a matsayin Gwamna a 2019. Yanzu haka Sanwo-Olu yana cikin Gwamnatin Ambode.

Bisa dukkan alamu tsohon Kwamishina a Gwamnatin Fashola watau Sanwo-Olu ne Tinubu yake marawa baya domin ya maye gurbin Ambode. Tuni dai kusan kaf Shugabannin Kananan Hukumomin Legas sun yi na’am da wannan.

Haka kuma akwai yiwuwar Majalisar dokokin Jihar ta Legas ta faa shirin tsige Gwamna Akinwumi Ambode bayan ganin ya yanki fam din takarar kujerar Gwamna a makon nan. Gwamna dai ya karyata wannan magana na tsige sa.

KU KARANTA: PDP na neman karbe Legas daga hannun Jam'iyyar APC

Vanguard ta rahoto cewa Gwamna Ambode na kokarin tsige Kakakin Majalisar dokokin Legas watau Mudashiru Obasa wanda ‘Dan-gani-kashe-nin Tinubu ne. Yanzu haka kusan duka Shugabannin APC na tare da Sanwo-Olu.

Asali dai Asiwaju Bola Tinubu ne ya kawo Ambode kan kujerar mulki a 2015. Sai dai Tinubu yana ganin Ambode na kokarin kassara sa a siyasa don haka yake neman ganin APC ta tsaida wani ‘Dan takarar dabam a zabe mai zuwa.

Sai jiya ne dai Gwamna Ambode ya saye fam din sake takarar kujerar Gwamnan Jihar inda yake neman goyon bayan Jama’a su mara masa baya su sake zaben sa a 2019. Ana tunani dai PDP kuma ta tsaida Femi Otedola Gwamna a 2019.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel