Gwamnatin Buhari ta zama tamkar mafaka ga tatattun barayin Najeriya - Tsohon kakakin APC

Gwamnatin Buhari ta zama tamkar mafaka ga tatattun barayin Najeriya - Tsohon kakakin APC

- Tsohon mai magana da yawun APC yayi kaca-kaca da gwamnatin Buhari

- Gwamnatin Buhari ta zama tamkar mafaka ga tatattun barayin Najeriya in ji shi

Tsohon mai magana da yawun jam'iyya mai mulki ta All Progressives Congress (APC), Kwamared Timi Frank yayi kaca-kaca da gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari, inda ya kamata ta da tamkar wata matattara ta tatattun barayin Najeriya da suka kware wajen cin hanci da rashawa.

Gwamnatin Buhari ta zama tamkar mafaka ga tatattun barayin Najeriya - Tsohon kakakin APC

Gwamnatin Buhari ta zama tamkar mafaka ga tatattun barayin Najeriya - Tsohon kakakin APC
Source: Depositphotos

KU KARANTA: An nemi wani babban jami'in soja an rasa a Najeriya

Kwamared Frank dai yayi wannan kalamin ne a cikin wata sanarwar da ya fitar ya kuma rabawa manema labarai a garin Abuja ranar Talata inda yace abun takaici ne yadda gwamnati da hukumomin da ke ikirarin yakar cin hanci da rashawa ke kokarin kare dukkan wani mai laifi indai ya cikin jam'iyyar APC.

Legit.ng ta samu haka zalika cewa Kwamared Frank ya kara da yin martani ga shugaban kwamitin shawara da garambawul na Shugaba Buhari watau Farfesa Itse Sagay a wata fira da akayi da shi inda yake cewa wai shugaba Buhari yana sane yake yin sako-sako da barayin domin ya samu ya lashe zaben sa na 2019.

A wani labarin kuma, Kamfanin sadarwar nan na MTN a Najeriya ya maka babban bankin na Najeriya watau Central Bank of Nigeria (CBN), da kuma Antoni Janar na kasar kuma ministan shari'a a gwamnatin shugaba Buhari kotu yana neman a bi masa hakkin sa.

Kamar dai yadda muka samu, shi dai kamfanin a ranar Litinin din da ta gabata ne ya shigar da karar kotu a garin Abuja, yana kalubalantar matakin da gwamnatin Najeriya ta kakaba masa.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel