Ana wata-ga wata: Ana zargin Cif Bola Tinubu da badakalar Naira biliyan 160

Ana wata-ga wata: Ana zargin Cif Bola Tinubu da badakalar Naira biliyan 160

- Ana zargi Cif Bola Tinubu da badakalar Naira biliyan 160

- Ance kamfanin sa ne yaki biyan kudin haraji

- PDP ta zargi EFCC da zama karen farautar APC

Babbar jam'iyyar adawa a Najeriya ta Peoples Democratic Party (PDP) ta nuna bukatar ta na ganin cewa hukumar nan ta gwamnatin tarayya dake yaki da cin hanci da rashawa ta Economic and Financial Crimes Commission (EFCC) ta binciki Cif Bola Ahmad Tinubu.

Ana wata-ga wata: Ana zargi Cif Bola Tinubu da badakalar Naira biliyan 160

Ana wata-ga wata: Ana zargi Cif Bola Tinubu da badakalar Naira biliyan 160
Source: Depositphotos

KU KARANTA: Ba maganar na'urar tantance katin zabe a 2019 - Fadar Shugaban kasa

Jam'iyyar ta PDP dai ta ce akwai bukatar a bincikin j=daya daga cikin jigogin jam'iyyar ta APC bisa zargin wani kamfanin da ke da alaka ta kusa da shi da badakalar kin biyan kudaden harajin sa da suka kai na Naira biliyan 160.

Legit.ng ta samu cewa jam'iyyar ta PDP ta cigaba da cewa wannan dai zai iya zama manuniya ga daukacin al'ummar kasar ga hukumar ta EFCC musamman ma ganin yadda ake ta zargin cewa ana anfani ne da ita kawai wajen muzgunawa 'yan adawa.

A wani labarin kuma, Babban kwamitin amintattu na jam'iyyar adawa a Najeriya ta Peoples Democratic Party (PDP), ya ce tuni yayi nisa wajen ganin ya kwantar da dukkan wata fitina da ka iya tasowa zaben fitar da gwanin dan takarar jam'iyyar na shugaban kasa a ranar 6 ga watan Okotoba mai zuwa.

Shugaban kwamitin amintattun, Sanata Walid Jibrin shine ya sanar da hakan a garin Abuja, ranar Litinin din da ta gabata inda ya bayyana cewa kawo yanzu dai suna ta kokarin ganin 'yan takarar dukkan su sun amince da sasancin da zai fito da mutum daya a tsakanin su.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel