Gwamnatin tarayya ta shimfida wa jihohi sharuda wajen cika musu kudaden Paris Club

Gwamnatin tarayya ta shimfida wa jihohi sharuda wajen cika musu kudaden Paris Club

A ranar Talata, 11 ga watan Satumba gwamnatin tarayya ta shimfida wa jihohin kasar sharuddan da sai kowace ta cika kafin a ba ta sauran cikon kudaden Paris Club tukunna.

Sauran cikon da tarayya za ta raba wa jihohin sun kai kimanin naira biliyan 823.5, wanda za a ba kowace jiha dala daya a kan naira 306.25.

Kakakin ma’aikatar harkokin kudade, Hassan Dodo ne ya bayyana haka. Ka’idojin da ya lissafa sun hada da tilastawa jiha bayar da fifiko wajen biyan albashi da kudaden da kuma sauran batutuwan da suka shafi biyan alawus da kuma kudaden bashi na ma’aikata da kudaden.

Sauran ka’idojin sun hada da biyan lamunin da jihohi suka ci daga gwamnatin tarayya a bisa gudanar da ayyukan da ke cikin kasafin kudin da jihohin suka ce sun karbi lamunin ne domin su yi ayyukan.

Gwamnatin tarayya ta shimfida wa jihohi sharuda wajen cika musu kudaden Paris Club

Gwamnatin tarayya ta shimfida wa jihohi sharuda wajen cika musu kudaden Paris Club
Source: Depositphotos

Wadannan lamuni dai ana maganar tun na cikin shekarar 2016. Sannan kuma akwai sharadin biyan kudaden takin zamani da suka karba daga gwamnatin tarayya, a karkashin Shirin Raba Takin Zamani na Ofishin Shugaban Kasa.

An kuma gindaya wa jihohi cewa su nuna da gaske su ke yi wajen kokarin gudanar da ayyukan Hukumar Samar da Ilmin Bai Daya, wato UBEC.

KU KARANTA KUMA: Dogara ya sanar da hukuncinsa na sake neman takara

Dodo ya ce wadannan bayanai ne gwamnatin tarayya ke nema daga jihohi domin a san abin da kowace ta yi da kudaden da aka ba ta na baya, ta yadda za a auna cancantar ba ta sauran balas na kudaden Paris Club din da suka rage, wadanda a yanzu aka gindaya mata sharuddan da ake so jiha ta cika kafin samun kudaden tukunna.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel