Gwamnatin Buhari ta shirya tsaf don tafka magudin zabe a 2019 - Wike

Gwamnatin Buhari ta shirya tsaf don tafka magudin zabe a 2019 - Wike

- Gwamnan jihar Ribers, Nyesome Wike ya karfafa zargin cewa kin akwai shirye shiryen da Buhari ya ke yi na tafka magudi a babban zabe na 2019 da ke gabatowa.

- Wike ya bayyana cewa makircin APC da gwamnatin tarayya shine rubuta sakamakon zabe, amma ba bin kadin abinda jama'a suke so ba.

- Ya jaddada muhimmancin kasashe ketare na daukar mataki akan jami'an gwamnatin APC ta hanyar dakatar da takardun basu izinin shiga kasashen su

Gwamnan jihar Ribers, Nyesome Wike ya karfafa zargin cewa kin amincewar da Buhari yayi na sanya hanu a dokar sake fasalin gudanar da zabe, na daga cikin hanyoyin tafka magudi a babban zabe na 2019 da ke gabatowa.

A cikin wata zantawa da akayi da shi a Fatakwal, Wike ya bayyana cewa makircin APC da gwamnatin tarayya shine rubuta sakamakon zabe, amma ba bin kadin abinda jama'a suke so ba.

Ya ce: "Me ya sa har yanzu shugaban kasa bai sanya hannu a dokar sake fasalin gudanar da zabe ba? Tsoron me ya ke ji? Me ake nufi da yin kuskure a ciki? Ikon Allah! Ace kuskuren da ka gaza gani a cikin wata daya, shi ne yau zaka ce ka gano kuskure a ciki? Shin wannan bai isa ya zama aya ga yan Nigeria cewa basu shirya gudanar da zabe ba?

KARANTA WANNAN: Mai gadi ya shiga halin ha-ula'i bayan da aka kamashi yana cire allunan tallar APC

Gwamnatin Buhari ta shirya tsaf don tafka magudin zabe a 2019 - Wike

Gwamnatin Buhari ta shirya tsaf don tafka magudin zabe a 2019 - Wike
Source: Depositphotos

"Tuggu da makircin da suka shirya shine rubuta sakamokon zabe, in yaso sai suka abinda zai faru. Da yawan su da suka bar PDP suka koma APC haka suke sanar da ni, dan uwana, cikin kwarin guiwa na ke sanar da kai wannan maganar, mutanen nan ba su shirya yin zabe ba."

Gwamnan ya yi nuni da cewa gwamnatin APC da jami'an tsaro ba zasu taba yin nasara a zaben jihar Rivers ba.

Ya ce: "A jihata, makircinsu ba zai yi tasiri ba. Na san za su kashe mutane da dama, zan iya tabbatar maka da hakan, za su kashe ire irenmu da yawa, amma babu matsala, idan har wannan ne tsarinsu, to mu kuma zamu fansar da rayukanmu akan kare jiharmu."

Gwamna Wike ya jaddada muhimmancin gwamnatocin kasashe ketare, da su dau mataki akan jami'an gwamnatin APC da suke tarwatsa demokaradiya da take dokokin kasa, ta hanyar dakatar da takardun basu izinin shiga kasashen su.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Tags:
Mailfire view pixel