EFCC ta kammala gabatar da hujjojin cin hanci a kan tsohon gwamnan PDP

EFCC ta kammala gabatar da hujjojin cin hanci a kan tsohon gwamnan PDP

- Hukumar yaki da cin hanci (EFCC) ta kammala gabatar da hujjar cin hanci a kan tsohon gwamna Rasheed Ladoja

- EFCC na zargin Ladoja da hada kai da wani mutum, Akanbi, da badakalar kudi biliyan N1.9bn

- Lauyan Ladoja ya ce zasu sanar da kotu cewar babu laifi a kan tsohon gwamnan

A yau, Talata, ne hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) ta kammala gabatar da hujjojin cin hanci a kan tsohon gwamnan jihar Oyo, Rasheed Ladoja, a gaban kotun tarayya dake Legas.

Ana tuhumar tsohon gwamna Ladoja da kwamishinansa na kudi, Waheed Akanbi, da badakalar kudi da yawansu ya kai biliyan N4.7bn daga asusun jihar Oyo.

A yayin da kotun ta zauna a yau, Talata, lauyoyin dake kare wadanda aka tuhuma sun sanar da kotu cewar wadanda suke karewar basu da laifi.

EFCC ta kammala gabatar da hujjojin cin hanci a kan tsohon gwamnan PDP

Rashidi Ladoja
Source: Depositphotos

An fara gurfanar da Ladoja da Akanbi a gaban kotun mai shari'a, Mohammed Idris, a ranar 14 ga watan Disamba na shekarar 2016.

Sai dai dukkan su sun musanta zargin tuhumar da ake masu.

Mai shari'a Idris ya daga cigaba da sauraron karar zuwa ranar 27 ga watan Satumba domin bayyana matsayin kotu a kan hujjojin da kowanne yanki ya gabatar.

DUBA WANNAN: Gwamnan APC ya amince da fitar da biliyan biliyan N19.8 don biyan bashin albashin wata 4

A wani labarin Legit.ng, kun ji cewar gwamnan jihar Zamfar, Abdulaziz Yari, ya bayyana niyyarsa ta tsayawa takarar Sanata da zai wakilicin yammacin Zamfara a majalisar dattijai.

Sai dai a yayin da wasu ke ganin gwamna Yari zai fafata neman kujerar ne da tsohon maigidansa, Sanata Abdullahi Sani Yarima, sai ga shi jaridar Tribune ta rawaito cewar Yariman ya janyewa gwamna Yari takarar kujerar sanatan yankin da suka fito, yammacin jihar Zamfara.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel