Dogara ya sanar da hukuncinsa na sake neman takara

Dogara ya sanar da hukuncinsa na sake neman takara

Kakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara ya sanar da kudirinsa na sake neman takara a majalisar wakilai.

Sanarwan Mista Dogara na kunshe ne a cikin wata sanarwa daga kakakinsa, Turaki Hassan, jaridar Premium Times ta ruwaito.

Sai dai Hassan bai bayyana a wace jam’iyya bace kakakin majalisar wakilan zai nemi takara ba, imma a jam’iyyarsa ta yanzu All Progressives Congress (APC) ko kumaa wata chan daban.

Ya bayyana hakan ne a maraiucen ranar Talata, 11 ga watan Satumba yayinda yake jawabi ga al’umman mazabarsa da suka zo don su bukaci ya sake takara.

Dogara ya sanar da hukuncinsa na sake neman takara

Dogara ya sanar da hukuncinsa na sake neman takara
Source: UGC

Dogara ya kuma yi godiya ga tarin goyon bayan da al’umman mazabarsa ke basa, cewa sunyi tattaki daga kananan hukumomin Bogoro, Dass da Tafawa Balewa dake jihar Bauchi zuwa Abuja don kawai su karfafa masa gwiwar saketakara.

KU KARANTA KUMA: Najeriya ta zargi Switzerland da masaniya kan kudaden da Abacha ya boye

A halin da ake ciki, Legit.ng ta rahoto cewa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a ranar Talata, 11 ga watan Satumba ya bayyana cewa yan siyasa masu rauni sun bar jam’iyyar All Progressives Congress, (APC).

Buhari na hannunka mai sanda ne ga yan siyasa da dama da suka sauya sheka daga jam’iyyar zuwa jam’iyyun adawa.

Yayi maganan ne yayinda ya karbi fam din sake tsayawa takara da kungiyar Nigeria Consolidation Ambassador Network (NCAN) ta siya masa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel