An kwato N11.1m na cin hanci da wasu 'yan sanda suka karba

An kwato N11.1m na cin hanci da wasu 'yan sanda suka karba

- Hukumar 'yan sanda ta kwato N11.1 miliyan na cin da yan sandan suka karba daga hannun jama'a

- Tuni hukumar 'yan sandan ta mayarwa mutanen kudadensu kana ta hukunta 'yan sandan da suka karbi cin hancin

- Hukumar ta kuma shawarci jama'a su rika kai karan 'yan sandan da suka gani yana karbar cin hanci

Sashin sauraron korafin jama'a na hukumar 'yan sandan Najeriya (PCRR) ta sanar da cewa hukumar ta kwato N11.1 miliyan da jami'an 'yan sanda suka karba a matsayin cin hanci daga mutane daban-daban.

Shugaban sashin, ACP, Abayomi Sogunle, ne ya bayyana hakan a ranar Talata a garin Osogbo, yayin wata taron wayar da kan jama'a da hukumar 'yan sanda ta shirya.

Sogunle ya kuma ce an mayarwa mutanen da aka karba kudin abinsu.

A cewarsa, hukumar ta kori sama da 'yan sanda 10 da aka samu da saba dokan aiki a shekaru biyu da suka wuce.

DUBA WANNAN: Fadan sarkin musulmi tayi tsokaci kan hatsarin 'dan Sultan

Ya ce ya ziyarci jihar ne saboda ya wayar da kan jama'a domin su rika kai karar duk wani jami'in dan sanda da suka gano yana saba dokar aiki musamman a yanzu da ake fuskantar zabe a jihar.

Jami'in dan sandan ya ce hukumar ba za ta amince da duk wani rashin da'a ba daga wani dan sanda saboda ta kare kima da mutuncin hukumar a Najeriya.

Sogunle ya ce hukumar za ta duba duk wani korafi da jama'a suka shigar saboda dawo da darajar hukumar a idanun mutane.

Ya kuma tunatar da 'yan sanda suyi kokari wajen magance bata gari da abubuwan da iya tayar da zaune tsaye a duk inda suke aiki.

Daga karshe, Sogunle ya tabbatar wa al'ummar jihar cewa hukumar za tayi kokarin ganin an gudanar da sahihiyar zabe kuma cikin zaman lafiya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel