Obasanjo na neman a halasta amfani da wiwi da sauran kwayoyi a Afrika

Obasanjo na neman a halasta amfani da wiwi da sauran kwayoyi a Afrika

- Cif Olusegun Obasanjo ya shawarci gwamnatocin kasashen Afirka su halasta amfani da wiwi da wasu miyagun kwayoyi idan suna son a rage safarar su

- Tsohon shugaban kasa, kuma ya yi kira ga gwamnatocin su mayar da hankali kan bawa masu amfani da kwayoyi kulawa a asibitoci a maimakon gidan yari

- Obasanjo ya ce kasashen duniya da yawa sun halasta amfani da wiwi saboda dokokin da aka kafa basu hana amfani dashi

Tsohon shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo ya shawarci kasashen Afirka ta yamma suyi garambawul ga dokokin hana shan kwayoyi ta yadda za su halasta shan kwayoyi idan har suna son magance matsalar ta'amuli da miyagun kwayoyin.

Ya kuma shawarci gwamnatocin kasashen su mayar da hankali kan bayar da kulawa ta musamman ga wadanda miyagun kwayoyi ya zama musu abin dogaro a rayuwa.

Obasanjo na neman a halasta amfani da wiwi, kodin da koken a Afrika

Obasanjo na neman a halasta amfani da wiwi, kodin da koken a Afrika
Source: Getty Images

A wata hira da akayi da shi kafin ya gabatar da sabon shirin magance matsalar ta'amuli da miyagun kwayoyi a Senegal, Mr Obasanjo ya shawarci mahukunta su mayar da hankali kan yaki da masu safarar miyagun kwayoyin.

DUBA WANNAN: Fadan sarkin musulmi tayi tsokaci kan hatsarin 'dan Sultan

Obasanjo ya ce ana samun karuwar masu shan kwayoyi kamar hodar iblis, koken da amphetamine duk da tsauraran matakan yaki da fatauci da miyagun kwayoyin.

Wannan shawarar ta Obasanjo ga kasashen Afirka ta yamma yana zuwa ne bayan wasu kasashen duniya sun fara halastawa jama'a amfani da wasu kwayoyi musamman ganyen wiwi saboda haramtawar da akayi baya hana mutane amfani dashi.

Canada ta hallasta amfani da ganyen wiwi a watan Yunin 2018 kuma galibin jihohi a Amurka sun halasta amfani da wiwi domin nishadi da kuma asibitoci domin magance wasu cututukan.

Obasanjo ya bayar da wadandan shawarwarin ne karkashin kwamitin da ya ke jagora kan Magance yaduwar amfani da miyagun kwayoyi a Afirka ta yamma. Sai dai kwamitin shawara kawai za ta iya bayar, yanzu ya rage gwamnatocin su dauki matakin halastawa ko akasin haka.

Tsohon shugaban kasan kuma ya ce gidan yari bata gyara halin mutane, hasali ma kangarar da mutane ta ke.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel