Tirka-Tirka: Hamshakin attajiri, Otedola, zai yi takara a PDP da Ambode

Tirka-Tirka: Hamshakin attajiri, Otedola, zai yi takara a PDP da Ambode

Attajirin dan kasuwa kuma Ciyaman din Forte Oil Plc, Femi Otedola, ya amsa gayyatar da aka yi masa na takarar gwamna a jihar Legas karkashin jam'iyyar PDP.

Tsohon dan jarida, mai wallafa mujjalar Ovation, Dele Momodu ne ya bayar da wannan sanarwar a shafinsa na Twitter inda ya ce Mr Otedola ya tabbatar masa cewa zaiyi takarar.

Tirka-Tirka: Hamshakin attajiri, Otedola, zai yi takara a PDP da Ambode

Tirka-Tirka: Hamshakin attajiri, Otedola, zai yi takara a PDP da Ambode
Source: UGC

Wannan na nuna cewa hamshakin dan kasuwan zai kara da gwamna Akinwunmi Ambode na jam'iyyar APC a zaben shekarar 2019 mai zuwa.

DUBA WANNAN: Zaben fidda gwani: Shehu Sani da wasu 'yan takara 14 sun yiwa APC tawaye a Kaduna

Ga abinda Momodu ya rubuta: "Yanzu-Yanzu: Za'a sha kallo a zaben 2019 a jihar Legas. PDP ta bawa Femi Otedola tikitin takarar gwamna. Ya amince zaiyi takarar kamar yadda ya tabbar min."

Legit.ng ta ruwaito cewa gwamna Akinwunmi Abmbode ya bayyana niyyarsa na sake tsayawa takarar karkashin jam'iyyar APC.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel