Da duminsa: Gwamnan APC ya amince da fitar da biliyan N19.8b don biyan albashin watan 4

Da duminsa: Gwamnan APC ya amince da fitar da biliyan N19.8b don biyan albashin watan 4

Gwamnan jihar Osun, Rauf Aregbesola, ya amince da fitar da biliyan N19.8bn adomin biyan ma’aikata da ‘yan fansho bashin hakkokinsu da suke bin jihar na tsawon wata 4.

A sanarwar da kwamishinan kudi na jihar Osun, Bola Oyebamiji, ya bayar a yau, Talata, y ace gwamna Rauf Aregbesola ya amince da fitar da biliyan N19.8bn domin a biya ma’aikata da ‘yan fansho bashin albashin wata 4 da suke bin jihar.

A ranar litinin da ta makon jiya ne jam’iyyar PDP ta gudanar da wani taro a “Legacy House” dake kan titin Shehu Shagari a garin Abuja, domin tattauna yadda zata tunkari zaben gwamnan jihar Osun da za a yi cikin wannan watan da muke ciki.

Da duminsa: Gwamnan APC ya amince da fitar da biliyan N19.8b don biyan albashin watan 4

Gwamna Rauf Aregbesola
Source: Depositphotos

Yayin taron, shugabancin jam’iyyar PDP ya kafa kwamitin mutane 22 karkashin jagorancin shugaban majalisar dattijai, Bukola Saraki, da take saka ran zai samar da hanyoyin da zasu kai ta ga nasara.

Za a yi zaben gwamna a jihar Osun ranar 22 ga watan Satumbar da muke ciki.

DUBA WANNAN: 2019: Surukin Buhari ya sayi fam din takarar gwamna a APC

Jam’iyyar APC ce ke mulkin jihar ta Osun yanzu haka, karkashin jagorancin gwamna Ogbeni Rauf Aregbosla.

Za a fafata a zaben na ranar 22 ga wata tsakanin dan takarar jam’iyyar APC,Gboyega Oyetola , da kuma na PDP, Sanata Ademola Adeleke.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel